Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Pound - A turance tana nufin kirɓa. Misali; Za mu kirɓa sakwara a ranar bikin da yardar Allah. HAU; Kirɓa (Tana nufin daka abu sosai a cikin turmi)
Pound and Crush something - A turance tana nufin dandaƙa. Misali; Za mu dandaƙa geron kafin mu yi kunu da shi. HAU: Dandaƙa (Tana nufin daka abu har ya zama gari)
Pounding corn for pay - A turance tana nufin dakau. Misali; Matar Ado dakau take yi a unguwarsu. HAU: Dakau (Tana nufin yin daka a matsayin sana'a)
Powder - A turance tana nufin hoda. Misali; An zubo hoda kala-kala a kayan lefen Tsahare. HAU; Hoda (Tana nufin gari mai laushi da mata ke shafawa a fuska don yin ado, akwai ja akwai fara da sauransu)
Power/Authority - A turance tana nufin iko. Misali; Shugabanni su ke da iko a kan mabiyansu. HAU; Iko (Tana nufin ƙarfi ko isa)
Praise - A turance tana nufin kirari. Misali; A kodayaushe akan yi wa mafarauta kirari kafin su tafi farauta. HAU; Kirari (Tana nufin maganganun da ake yi wa mutum ko mutane don kwarzantawa ko kambamawa)
Presents of foodstuffs given by parents of bride to parent of groom - A turance tana nufin gara. Misali; An yi wa amaryar gara ta ban mamaki. HAU; Gara (Tana nufin kayan masarufi da iyayen mace ke haɗota da su bayan aure)
Press - A turance tana nufin danna. Misali; Ina ta danna ƙofar amma ta ƙi buɗuwa. HAU; Danna (Tana nufin amfani da hannu a ba da ƙarfi akan abu)
Prevent - A turance tana nufin hana. Misali; An hana zuwa makaranta a makare. HAU; Hana (Tana nufin ƙin ba da dama)
Price - A turance tana nufin farashi. Misali; Ana ta ƙarawa kaya farashi a kasuwa saboda karyewar tattalin arziƙi. HAU; Farashi (Tana nufin kuɗin abu)
1 5 6 7 8 9 10