Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Poison - A turance tana nufin dafi.
Misali; Dabbobin da suke da dafi suna da hatsari matuƙa.
HAU; Dafi (Tana nufin abin da ke iya kisa, zai iya kasancewa daga dabbobi ko wani abu daban)
Poison - A turance tana nufin guba.
Misali; Na sa wa ɓeraye guba jiya da yamma.
HAU; Guba (Tana nufin duk wani abin da zai iya kisa)
Police Service Commission (PSC) - Hukumar Aikin 'Yansanda
Polite - A turance tana nufin kintsattse.
Misali; Ai da ganinsa an ga kintsattse, don kamanninsa sun nuna haka.
HAU; Kintsattse (Tana nufin mutum mai kamala da nutsuwa)
Political Party - A turance tana nufin jam'iyya.
Misali; Dukkansu 'yan jam'iyya ɗaya ne.
HAU; Jam'iyya (Tana nufin zauren siyasa)
Poor, Destitute - A turance tana nufin faƙiri.
Misali; Idan za ka yi sadaka ka nemi faƙiri ka ba shi.
HAU; Faƙiri (Tana nufin talaka wanda ba shi da komai)
Portfolio & Debt Management Institute of Nigeria (PDMIN) - Cibiyar Naƙaltar Juya Dukiya da Bashi Ta Najeriya
Potash - A turance tana nufin kanwa.
Misali; Ki ɗan jefa kanwa a waken don ya yi laushi da wuri.
HAU; Kanwa (Tana nufin wani nau'in gishirin tabki mai ƙunshe da sinadarin sodium a ciki)
Potatoes - A turance tana nufin dankali.
Misali; Ina son dankali musamman soyayye.
HAU; Dankali (Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in abinci)
Poultry Association of Nigeria (PAN) - Ƙungiyar Makiwata Tsuntsaye Ta Najeriya