Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Pharmacists Council of Nigeria (PCN) - Hukumar Masana Magunguna Ta Najeriya
Phlegm From Throat - A turance tana nufin kaki. Misali; Mura ta sa yana ta kaki. HAU; Kaki (Tana nufin majinar da ake fitarwa daga maƙogwaro)
Photograph - A turance tana nufin hoto. Misali; Idan an gama taron za mu ɗauki hoto saboda tarihi. HAU; Hoto (Tana nufin taswira)
Pied Crow - A turance tana nufin hankaka. Misali; Ya kamo hankaka da ya fita farauta. HAU; Hankaka (Tana nufin tsuntsu mai launi biyu, ƙirjinsa fari sauran jikinsa baƙi)
Pile loads on top of one another - A turance tana nufin jibga. Misali; Na ga Habu ya jibga kaya a jikinsa wai sanyi yake ji. HAU; Jibga (Tana nufin ɗora kaya da yawa)
Pillar supporting a roof - A turance tana nufin ginshiƙi. Misali; Imani shi ne ginshiƙin addini. HAU; Ginshiƙi (Tana nufin jigo ko tushe)
Pimp - A turance tana nufin kawali. Misali; Cin fuska ne a ce wa mutum kawali don ba sana'ar mutanen kirki ba ce. HAU; Kawali (Tana nufin wanda yake haɗa mata masu zaman kansu da maza, kuma sukan ba shi wani kaso daga cikin kuɗin da suka samu)
Pimple / Boil - A turance tana nufin ƙurji. Misali: Wani ƙurji ya fito masa a fuska, wanda ya sa gurin ya kumbura. HAU: Ƙurji (Tana nufin ƙarami ko babban kumburi da ke fitowa a fata, wanda galibi ke ɗauke da ruwa ko mugunya)
Pipeline Professionals Association of Nigeria (PPAN) - Ƙungiyar Ƙwararrun Ma'aikatan Bututu Ta Najeriya
Pipelines & Products Marketing Company (PPMC) - Kamfanin Bututu da Jigilar Tataccen Mai
1 3 4 5 6 7 11