Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Imani - Tana nufin yarda, amincewa ko ba da amanna ɗari bisa ɗari.
Misali; Yarda da ƙaddara mai kyau ko mara kyau na ɗaya daga cikin rukunan imani.
ENG; Faith (A turance tana nufin imani)
Imitate - A turance tana nufin koyi.
Misali; Koyi da annabawa kyakkyawar ɗabi'a ce.
HAU; Koyi (Tana nufin kwaikwaya ko yin abinda wani ya yi)
Imitate - A turance tana nufin kwaikwaya.
Misali; Habu kukan doki yake kwaikwaya da na mage.
HAU; Kwaikwaya (Tana nufin yin abu kamar yanda na asali yake)
Imma - Tana nufin ko.
Misali; Ka zaɓi ɗaya, imma makarantar kwana ko ta je-ka-ka-dawo.
ENG; Either/Or (A turance tana nufin imma)
Impress - A turance tana nufin burge.
Misali; Samarin na ƙoƙarin yin komai don burge 'yan matan su.
HAU; Burge (Tana nufin ƙoƙarin janyo ra'ayi ko yardar wani)
In’ina - Tana nufin yin magana da ƙyar ko ana yi ana tsittsitsinkawa.
Misali; An ce shan ruwan tattabaru na sauƙaƙa in'ina.
ENG; Stuttering/ Stammering (A turance tana nufin in'ina)
Inability to come to the point; beating around the bush - A turance tana nufin ƙumbiya-ƙumbiya.
Misali: Ka daina ƙumbiya-ƙumbiya ka faɗi abin da kake nufi kai tsaye.
HAU: Ƙumbiya-ƙumbiya (Tana nufin yin magana ko bayani cikin karkacewa ba tare da zuwa kan ainihin batu kai tsaye ba)
Increase - A turance tana nufin ƙari ko ƙaruwa.
Misali; Farashin kaya ya ƙaru a wannan watan.
HAU; Ƙari (Tana nufin ƙara wani abu fiye da yadda yake a da).
Increase - A turance tana nufin ƙaru.
Misali; Yawan ɗalibai ya ƙaru a makarantar wannan shekara.
HAU; Ƙaru (Tana nufin ƙaruwa ko ƙara yawa).
Inda - Tana nufin gurin da abu yake.
Misali; Mukullin yana inda nake ajiye kayana.
ENG; Where (A turance tana nufin inda)