Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Loud Fuss - A turance tana nufin kwakwazo.
Misali; Tun safe Lami take kwakwazo don an ɗauke mata kuɗi a gidan suna.
HAU; Kwakwazo (Tana nufin hayaniya da hayagaga)
Louse / Lice -
A turance tana nufin kwarkwata.
Misali: Indo ta shafa wa yaranta maganin kashe kwarkwata a kansu.
HAU; Kwarkwata (Tana nufin ƙananan ƙwari da ke rayuwa a gashin kai ko jiki suna tsotsar jini)
Love portion smeared on the eye - A turance tana nufin ƙifil.
Misali: Wasu mutane sun yarda da cewa ƙifil na iya sa mutum ya ƙaunaci wani.
HAU: Ƙifil (Tana nufin wani magani ko haɗi da ake shafawa a ido domin jawo soyayya ko tasiri a kan wani)
Lover / Mistress -
Low mud platform outside compound - A turance tana nufin dakali.
Misali; Baba yana zaune a kan dakali da abokinsa suna hira.
HAU; Dakali (Tana nufin gini mai ɗan tudu da ake yi a ƙofar gida don zama)
Lower Back - A turance tana nufin ƙugu.
Misali: Ya ji ciwo a ƙugu bayan ya ɗauki kaya masu nauyi.
HAU: Ƙugu (Tana nufin sashen baya da ke tsakanin ƙirji da mazauni, wato ƙasan baya)
Lungs - A turance tana nufin huhu.
Misali; Shan taba yana illata huhu a wasu lokutan ma har a rasa rai.
HAU; Huhu (Tana nufin ɓangaren da ke sarrafa iska a jikin ɗan Adam)
Lying down -
A turance tana nufin kwanciya.
Misali; Bayan ya gama aiki ya samu gurin kwanciya domin ya huta.
HAU; Kwanciya (Tana nufin shimfiɗa jiki ko hutawa a kan gado, tabarma ko wani wuri)