Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Lock - A turance tana nufin kulle. Misali; Lokacin da muka je an kulle ƙofar saboda mun makara. HAU; Kulle (Tana nufin rufewa)
Locust bean - A turance tana nufin daddawa. Misali; Miyar kuka ta fi daɗi idan ta ji daddawa. HAU; Daddawa (Tana nufin sinadarin girki mai sa ƙamshi da armashin abinci)
Long metal horn blown in honour of an Emir - A turance tana nufin kakaki. Misali; Da ka ji kakaki to sarki ya fito daga fada. HAU; Kakaki (Tana nufin abin busa na ƙarfe wanda sarki kaɗai ake busawa)
Long pole used for canoeing or as roof pole of house -

A turance tana nufin kwangwala.

Misali; An sa kwangwala a kan rufin gidan Alaramma kafin a sa siminti.

HAU; Kwangwala (Tana nufin doguwar sanda da ake amfani da ita wajen tuƙa jirgin ruwa ko kuma a matsayin sandar da ake rufi a gidajen gargajiya)

Long sleeve worn as inner garment - A turance tana nufin jamfa. Misali; Ya sa jamfa mai gajeren hannu kalar makuba. HAU; Jamfa (Tana nufin rigar da ake sa wa a ƙasa kafin a ɗora babbar riga)
Looting in a noisy manner - A turance tana nufin ɓuruntu. Misali; Ɓera yana ta ɓuruntu a ɗakin Kaka. HAU; Ɓuruntu (Tana nufin ɓare-ɓare da hayaniya)
Lose Interest - A turance tana nufin gundura. Misali; Kallon wasan ƙwallon ƙafa ya gundure ni. HAU; Gundura (Tana nufin jin abu ya fita daga rai)
Losing Baby Teeth - A turance tana nufin famfara. Misali; Muntari yana famfara. HAU; Famfara (Tana nufin cirewar da haƙoran yara ke yi kafin na girma ya fito)
Lost - A turance tana nufin ɓata. Misali; Ina tunanin takalmin ya ɓata, don na duba ko ina ban ganshi ba. HAU; Ɓata (Tana nufin a nemi abu a rasa)
Loud Argument - A turance tana nufin hatsaniya. Misali; Mata da mijin sun yi hatsaniya har ta kai matar ta yi yaji. HAU; Hatsaniya (Tana nufin cacar baki ko cece-kuce)
1 5 6 7 8