Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Limping - A turance tana nufin ɗingishi.
Msali; Ɗingishi take yi saboda marurun da ya fito a ƙafarta.
HAU; Ɗingishi (Tana nufin yin tafiya ba daidai ba, ana yi ana dakatawa saboda dalilin ciwo a ƙafa ko wani abu daban)
Linguistics Association of Nigeria (LAN) - Ƙungiyar Masan Kimiyyar Harshe Ta Najeriya
Liniency/Pardon - A turance yana nufin sassauci ko yafiya.
Misali; An yi wa masu laifin afuwa.
HAU; Ahuwa (Yana nufin sassauci ko yafiya)
Lipstick - A turance tana nufin jan-baki.
Misali; Amaryar ta sha ado da jan-baki.
HAU; Jan-baki (Tana nufin abin shafawa a leɓe mai canja masa launi wanda mata ke amfani da shi)
Literature - A turance yana nufin Adabi.
Misali; Adabin Hausa yana da faɗi da rassa daban-daban.
HAU; Adabi (Yana nufin madubin duba rayuwar al'umma)
Litinin - Rana ce ta farko daga cikin ranakun mako.
Misali; Ranar Litinin zan fara zuwa makaranta.
ENG: Monday
Liver - A turance tana nufin hanta.
Misali; Farfesun hanta zan dafa a matsayin karin kumallo.
HAU; Hanta (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan ciki wadda ke tace jini da fitar da datti daga cikin jini)
Lizard -
A turance tana nufin ƙadangare.
Misali; Ƙadangare ya hau bangon ɗaki.
HAU; Ƙadangare (Tana nufin dabba mai rarrafe da ake yawan gani a bango ko ƙasa)
Local Authority Administrator - A turance tana nufin kantoma.
Misali; An naɗa baban su Sharif kantoma a ƙaramar hukumar Dala.
HAU; Kantoma (Tana nufin mai riƙon ƙwaryar shugabancin ƙaramar hukuma)
Local Government Council - Majilisar Ƙaramar Hukuma