Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Litinin - Rana ce ta farko daga cikin ranakun mako.
Misali; Ranar Litinin zan fara zuwa makaranta.
ENG: Monday
Liver - A turance tana nufin hanta.
Misali; Farfesun hanta zan dafa a matsayin karin kumallo.
HAU; Hanta (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan ciki wadda ke tace jini da fitar da datti daga cikin jini)
Local Authority Administrator - A turance tana nufin kantoma.
Misali; An naɗa baban su Sharif kantoma a ƙaramar hukumar Dala.
HAU; Kantoma (Tana nufin mai riƙon ƙwaryar shugabancin ƙaramar hukuma)
Local Government Council - Majilisar Ƙaramar Hukuma
Lock - A turance tana nufin kulle.
Misali; Lokacin da muka je an kulle ƙofar saboda mun makara.
HAU; Kulle (Tana nufin rufewa)
Locust bean - A turance tana nufin daddawa.
Misali; Miyar kuka ta fi daɗi idan ta ji daddawa.
HAU; Daddawa (Tana nufin sinadarin girki mai sa ƙamshi da armashin abinci)
Long metal horn blown in honour of an Emir - A turance tana nufin kakaki.
Misali; Da ka ji kakaki to sarki ya fito daga fada.
HAU; Kakaki (Tana nufin abin busa na ƙarfe wanda sarki kaɗai ake busawa)
Long sleeve worn as inner garment - A turance tana nufin jamfa.
Misali; Ya sa jamfa mai gajeren hannu kalar makuba.
HAU; Jamfa (Tana nufin rigar da ake sa wa a ƙasa kafin a ɗora babbar riga)
Looting in a noisy manner - A turance tana nufin ɓuruntu.
Misali; Ɓera yana ta ɓuruntu a ɗakin Kaka.
HAU; Ɓuruntu (Tana nufin ɓare-ɓare da hayaniya)
Lose Interest - A turance tana nufin gundura.
Misali; Kallon wasan ƙwallon ƙafa ya gundure ni.
HAU; Gundura (Tana nufin jin abu ya fita daga rai)