Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Leucoma - A turance tana nufin hakiya.
Misali; Hakiya ce ta fito masa a ido.
HAU; Hakiya (Tana nufin ciwon da ke fitowa a cikin ido)
Library Registration Council of Nigeria (LRCN) - Hukumar Ɗakunan Karatu Ta Najeriya
Licensed Electrical Contractors Association of Nigeria (LECAN) - Kungiyar Sahalallun 'Ƴankwangilar Lantarki Ta Najeriya
Lift and carry something heavy - A turance tana nufin cicciɓa.
Misali; Buhun simintin za mu cicciɓa mu kai saman benen.
HAU: Cicciɓa (Tana nufin ɗaukar abu mai nauyi)
Light - A turance tana nufin haske.
Misali; Haske ya mamaye ɗakin sakamakon kunna fitilar da Laure ta yi.
HAU; Haske (Tana nufin abin da ke fitowa idan rana ta fito kuma yake gushewa idan ranar ta faɗi)
Kishiyarta; Duhu
Limping - A turance tana nufin ɗingishi.
Msali; Ɗingishi take yi saboda marurun da ya fito a ƙafarta.
HAU; Ɗingishi (Tana nufin yin tafiya ba daidai ba, ana yi ana dakatawa saboda dalilin ciwo a ƙafa ko wani abu daban)
Linguistics Association of Nigeria (LAN) - Ƙungiyar Masan Kimiyyar Harshe Ta Najeriya
Liniency/Pardon - A turance yana nufin sassauci ko yafiya.
Misali; An yi wa masu laifin afuwa.
HAU; Ahuwa (Yana nufin sassauci ko yafiya)
Lipstick - A turance tana nufin jan-baki.
Misali; Amaryar ta sha ado da jan-baki.
HAU; Jan-baki (Tana nufin abin shafawa a leɓe mai canja masa launi wanda mata ke amfani da shi)
Literature - A turance yana nufin Adabi.
Misali; Adabin Hausa yana da faɗi da rassa daban-daban.
HAU; Adabi (Yana nufin madubin duba rayuwar al'umma)