Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Large - A turance tana nufin danƙwalele. Misali;Na siyowa kakata danƙwalelen goro a kasuwa. HAU;Danƙwalele (Tana nufin babba ko mai girma)
Large and round (of eyes, onions, or fruit) - A turance tana nufin ƙulu-ƙulu. Misali: Idanunsa sun yi ƙulu-ƙulu, sakamakon kukan da ya yi sosai. HAU: Ƙulu-ƙulu (Tana nufin abu mai girma kuma zagayayye, musamman idan ana magana a kan idanu, albasa, ko wasu ’ya’yan itatuwa)
Large Edible Toad - A turance tana nufin ƙozo. Misali: Masunta sun kama ƙozo a bakin ruwa da yamma yayin da suke kamun kifi. HAU: Ƙozo (Tana nufin babban kwaɗo)
Large hen - A turance tana nufin daƙwalwa. Misali; Kazar daƙwalwa ce don ta ƙosar da mu. HAU; Daƙwalwa (Tana nufin babbar kaza ma'abociyar tsoka)
Large hoe with wide blade - A turance tana nufin garma. Misali; Gatari ba zai yi aikin nan ba sai dai a sa garma. HAU; Garma (Tana nufin ƙaton gatari mai faffaɗan kai)
Large Mass - A turance tana nufin dafifi. Misali; Mutane sun yi dafifi a wajen kallon wasan kalankuwa. HAU; Dafifi (Tana nufin taruwar jama'a da yawa)
Large millipede -

A turance tana nufin ƙadandoniya.

Misali; Yara sun ga ƙadandoniya a bayan gida.

HAU; Ƙadandoniya (Tana nufin wani ƙwaro mai ƙafafu da yawa)

Large needle - A turance tana nufin basilla. Misali; Na yi amfani da basilla na ɗinke buhun kayana. HAU; Basilla (Tana nufin allura babba da ake amfani da ita wajen ɗinke buhu ko ƙwarya da sauransu)
Large noise -

A turance tana nufin kwaramniya.

Misali; An ji kwaramniya a kasuwa lokacin da mutane suka taru.

HAU; Kwaramniya (Tana nufin hayaniya mai ƙarfi ko girgiza kunne)

Large Stallion - A turance tana nufin ingarma. Misali; Dokin yarima ingarma ne. HAU; Ingarma (Tana nufin babban doki ko gabjejen mutum)
1 2 3 4 8