Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Jimiri - Tana nufin haƙuri da juriya. Misali; Duk wanda ya yi jimirin yin aiki zai samu kyakkyawan sakamako. ENG; Endurance/Patience (A turance tana nufin jimiri)
Jinga - Tana nufin yarjejeniyar biyan kuɗi. Misali; Mun yi jinga da shi zai biya ni da zarar na kammala aikin. ENG; Wages (A turance tana nufin jinga)
Jingim - Tana nufin adadi mai yawa. Misali; Ya tara kayan wanki jingim a ɗaki, da ƙyar zai iya wankewa shi kaɗai. ENG; Plentiful (A turance tana nufin jingim)
Jingina - Tana nufin bayar da ajiyar wata kadara domin rancen kuɗi da zimmar idan aka biya kuɗin sai a karɓa. Misali; Gidansa ya bayar jingina a banki ya karɓo bashin. ENG; Deposit given as a pledge for money borrowed (A turance tana nufin jingina)
Jini - Tana nufin sinadarin ruwa mai launin ja wanda zuciya take harbawa sassan jiki, yana ƙunshe da abubuwan da jiki ke buƙata domin rayuwa. Misali; Likita ya ce sai an ƙara masa jini leda ɗaya. ENG; Blood (A turance tana nufin jini)
Jiniya - Tana nufin ƙarar da motar asibiti ko ta 'yan kwana-kwana ko 'yan siyasa ke ɗauke da ita. Ƙarar na nuni da cewa abu ne na gaggawa ya faru, ko gobara, ko an ɗauko mara lafiya da sauransu. Misali; Na jiyo jiniya, da alama 'yan kwana-kwana sun zo gurin gobarar. ENG: Siren (A turance tana nufin jiniya)
Jinjina - Tana nufin gaisuwar ban-girma. Misali; Shugaban sojojin yana shigowa ɗakin taron aka yi masa jinjina. ENG; Saluting a superior (A turance tana nufin jinjina)
Jinjiri - Tana nufin jariri. Misali; Jinjiri aka haifa masa shekaran jiya. ENG; Infant (A turance tana nufin jinjiri) Kishiyarta; Jinjinniya
Jinkiri - Tana nufin dakatawa ko ɗaukan lokaci. Misali; An samu jinkiri wajen fitar da sakamakon jarrabawar saboda wasu ƙwararan dalilai. ENG; Delay (A turance tana nufin jinkiri)
Jinya - Tana nufin kwanciya a dalilin rashin lafiya ko kula da mara lafiya. Misali; Ya shekara guda yana jinya sakamakon haɗarin. ENG; Nursing (A turance tana nufin jinya)
1 6 7 8 9 10