Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Jiha - Tana nufin wani yanki daga cikin ƙasa.
Misali; An ƙirƙiri sabuwar jiha a ƙasar Najeriya.
ENG; State (A turance tana nufin jiha)
Jihadi - Tana nufin yaƙi don ɗaukaka addinin musulunci.
Misali; Sahabbai sun yi jihadi don ɗaukaka addinin musulunci.
ENG; Holy war to spread Islam (A turance tana nufin jihadi)
Jijiya - Tana nufin hanyar jini a jikin mutum ko dabba.
Misali; Allurar jijiya aka yi masa saboda zafin zazzaɓin.
ENG; Vein (A turance tana nufin jijiya)
Jijjiga - Tana nufin girgizawa.
Misali; Sai an jijjiga maganin sannan ake sha.
ENG; Shake (A turance tana nufin jijjiga)
Jika - Tana nufin yaro ko yarinyar da ɗa ko 'ya suka haifa.
Misali; Maƙoci na ya yi jika, jiya 'yarsa ta haihu.
ENG; Grandchild (A turance tana nufin jika)
Jiki - Tana nufin sassa gaba ɗaya daga kai zuwa ƙafa.
Misali; Ya sha maganin ciwon jiki ya kwanta.
ENG; Body (A turance tana nufin jiki)
Jima’i - Tana nufin saduwa tsakanin mace da namiji.
Misali; Cututtukan sanyi na da nasaba da jima'i a lokuta da dama.
ENG; Sexual Intercourse (A turance tana nufin jima'i)
Jimada Awwal - Tana nufin wata na biyar a watannin musulunci.
Misali; A watan Jimada Awwal za a yaye ɗaliban.
ENG; Fifth month of Islamic calendar (A turance tana nufin jimada awwal)
Jimilla - Tana nufin sakamako na bai ɗaya.
Misali; Idan an haɗa kudina da naka za a samu jimillar dubu goma sha biyu.
ENG; Sum Total (A turance tana nufin jimilla)
Jimina - Tana nufin nau'in tsutsuwa mai dogon wuya wadda ke yin ƙwai.
Misali; Akwai jimina a gidan adana namun dajin da ke garinmu.
ENG; Ostrich (A turance tana nufin jimina)