Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Jela - Tana nufin bindi.
Misali; Jakin yana da doguwar jela.
ENG; Tail (A turance tana nufin jela)
Jemage - Tana nufin dabba mai tashi sama wadda ba ta taɓa ƙasa.
Misali; Akwai jemage a kan bishiyar ƙofar gida.
ENG; Bat (A turance tana nufin jemage)
Jewa - Tana nufin je-ka-ka-dawo.
Misali; Na gan shi yana ta jewa saboda tashin hankali.
ENG; Going to and fro (A turance tana nufin jewa)
Jibga - Tana nufin ɗora kaya da yawa.
Misali; Na ga Habu ya jibga kaya a jikinsa wai sanyi yake ji.
ENG; Pile loads on top of one another (A turance tana nufin jibga)
Jibi - Tana nufin ranar da ke bin gobe.
Misali; Jibi za a fara bikin kuma sai an jera sati ana yi.
ENG; Day After Tomorrow (A turance tana nufin jibi)
Jidali - Tana nufin rikici ko ɗawainiya.
Misali; Ya janyo wa kansa jidali tunda ya auri yarinyar nan.
ENG; Struggle/Trouble (A turance tana nufin jidali)
Jiddin - Tana nufin kodayaushe.
Misali; Ai Jiddin yana masallaci tunda Allah ya shirye shi.
ENG; Always (A turance tana nufin jiddin)
Jido - Tana nufin ɗebo kaya daga wani guri zuwa wani gurin.
Misali; Mun jido kayan daga tsohon gida zuwa sabo.
ENG; Removal of things to another location (A turance tana nufin jido)
Jigida - Tana nufin dutsinan ado da mata ke ɗaurawa a ƙugu.
Misali; Tana da jigida mai hawa goma.
ENG; Ornamental beads worn around hips by women (A turance tana nufin jigida)
Jigila - Tana nufin kai wa da komowa (kai-komo).
Misali; Kamfanonin jiragen sama na ta jigilar alhazai daga ƙasashe daban-daban.
ENG; Going back and forth (A turance tana nufin jigila)