Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Jariri - Tana nufin wanda ba a daɗe da haifa ba.
Misali; An tsinci jariri a unguwarmu.
ENG; Infant (A turance tana nufin jariri)
Jarrabawa - Tana nufin gwaji.
Misali; Suna gama jarrabawa za a ba su hutu.
ENG; Examination (A turance tana nufin jarrabawa)
Jarumi - Tana nufin ƙaƙƙarfa ko jajirtacce.
Misali; Shi kaɗai ne jarumi a cikin gidan.
ENG; Brave (A turance tana nufin jarumi)
Jauje - Tana nufin abin kiɗa mai kama da kalangu.
Misali; A cikin kayan da suke kaɗawa har da jauje.
ENG; Drum similar to but larger than kalangu (A turance tana nufin jauje)
Jawabi - Tana nufin bayani a kan wani maudu'i.
Misali; A halin yanzu mai girma gwamna ne yake jawabi a ɗakin taron.
ENG; Speech (A turance tana nufin jawabi)
Jayayya - Tana nufin faɗi in faɗa.
Misali; Tun safe suke jayayya a kan kuɗi.
ENG; Controversy (A turance tana nufin jayayya)
Jaɓa - Tana nufin dabba mai kamar ɓera amma ta fi shi girma tana da dogon baki kuma tana wari.
Misali; Akwai jaɓa a ɗakin nan don na ji warinta da na shigo.
ENG; Stinking Shrew- Mouse (A turance tana nufin jaɓa)
Jealousy - A turance tana nufin kishi.
Misali; Matan wannan zamani na da matuƙar kishi wanda ya saɓawa shari'a.
HAU; Kishi (Tana nufin sosuwar zuciya da ɓacin ran da suke jawo fushi, a dalilin tarayyar da wani ya yi da wani, a kan abin da wanin ya keɓanta da son sa koma mallakarsa)
Jefi-jefi - Tana nufin ba kodayaushe ba.
Misali; Yana zuwa gaishe da kakarsa jefi-jefi.
ENG; Often (A turance tana nufin jefi-jefi)
Kishiyarta; A kai-a kai
Jego - Tana nufin shayar da jariri.
Misali; Indo jego take shi yasa ba za ta bi mu ba.
ENG; Suckling of Infant (A turance tana nufin jego)