Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Janar - Tana nufin babban muƙamin soja.
Misali; Ya kai matakin Janar a aikin soja yanzu.
ENG; General (A turance tana nufin janar)
Janareto - Tana nufin injin da ke bayar da wutar lantarki idan an sa masa fetur.
Misali; Rashin wuta ya sa janareto ya yi tsada matuƙa.
ENG; Generator (A turance tana nufin janareto)
Jangali - Tana nufin kuɗin harajin da ake biyawa shanu.
Misali; Malam Modibbo ya biya jangali da wuri wannan karon.
ENG; Cattle Tax (A turance tana nufin jangali)
Janjani - Tana nufin ɗaukan lokaci wajen cin abinci, wato ci a hankali a hankali.
Misali; Abdulhakim ya fiya janjani.
ENG; Slowness in Eating (A turance tana nufin janjani)
January - A turance yana nufin watan farko a shekara.
Misali; Bikin sabuwar shekara na kasancewa a ranar ɗaya ga watan Janairu.
HAU; Janairu (Watan farko ne a shekara)
Janye - Tana nufin jan abu daga muhallinsa.
Misali; An janye motar da ta lalace ta tare hanyar wucewa.
ENG; Drag Away (A turance tana nufin janye)
Jaraba - Tana nufin jin so mai tsanani.
Misali; Shan giya ya zama jaraba gare shi, sai ya sha yake jin daɗi.
ENG; Excessive Desire (A turance tana nufin jaraba)
Jarfa - Tana nufin tsagun fuska.
Misali; Jarfa, gadon gidansu ne.
ENG; Facial Markings (A turance tana nufin jarfa)
Jarida - Tana nufi takarda mai ƙunshe da rubutun labarai.
Misali; Dattijai na son karanta jarida don jin halin da duniya take ciki.
ENG; Newspaper (A turance tana nufin jarida)
Jarirai - Tana nufin jam'in jariri.
Misali; Kayan da gwamnati ta kawo na tallafin jarirai ne.
ENG; Infants (A turance tana nufin jarirai)