Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Jaje - Tana nufin taya alhini da tausayawa wanda wani abu mara daɗi ya same shi.
Misali; Shugaban ƙasa ya yi wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa jaje.
ENG; Sympathy (A turance tana nufin jaje)
Jajibere - Tana nufin kwana ɗaya kafin ranar biki (sallah ko wani shagali).
Misali; Yau jajiberen ƙaramar sallah.
ENG; Day before festival day (A turance tana nufin jajibere)
Jaka - Tana nufin abar da ake ratayawa a kafaɗa ko a riƙe a hannu, ana zuba kuɗi da kayayyaki a ciki.
Misali; A kasuwa aka sace mata jaka kuma duk kuɗinta suna ciki.
ENG; Bag (A turance tana nufin jaka)
Jakada - Tana nufin wakili.
Misali; An naɗa babanta jakadan Nageriya a ƙasar Niger.
ENG; Ambassador (A turance tana nufin jakada)
Jaki - Tana nufin dabba mai ƙafa huɗu wanda ake amafani da shi don ɗaukar kaya, yana da juriya sosai.
Misali; Malam Mudi yana wani tsohon jaki.
ENG; Donkey (A turance tana nufin jaki)
Jalla - Tana nufin Allah maɗaukakin sarki.
Misali; Allah jalla wa azza ne ya nufa za a yi ruwa mai yawa yau.
ENG; God (A turance tana nufin jalla)
Jallo - Tana nufin mazubin ruwa na duma.
Misali; Jauro ya shanye ruwan cikin jallo na, sai na ɗebo wani.
ENG; Gourd Water Bottle (A turance tana nufin jallo)
Jam’i - Tana nufin haɗuwar mutane don yin sallah.
Misali; Sun yi jam'i za su yi sallar azahar.
ENG; Congregation of people for joint prayer (A turance tana nufin jam'i)
Jam’iyya - Tana nufin zauren siyasa.
Misali; Dukkansu 'yan jam'iyya ɗaya ne.
ENG; Political Party (A turance tana nufin jam'iyya)
Jama’a - Tana nufin mutane da yawa.
Misali; Bikin ya tara jama'a daga sassan duniya daban-daban.
ENG; The Public (A turance tana nufin jama'a)