Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Haɓar Kada - Tana nufin hular gargajiya mai rufe kunnuwa wadda musamman fulani ke amfani da ita.
Misali; Samarin sun yi kwalliyar haɓar kada
ENG; Cotton cap with pointed flaps which covers ears worn especially by fulani (A turance tana nufin haɓar kada)
Haɓe - Tana nufin wanda ba bafulatani ba. Fulani kan kira wanda ba ɗan ƙabilarsu ba da wannan suna.
Misali; Abokin Jauro haɓe ne.
ENG; Hausa person who has no Fulani ancestry (A turance tana nufin haɓe)
Haɓo - Tana nufin zubar jini daga hanci.
Misali; Tun safe yake haɓo, ko za a kai shi asibiti ne?
ENG; Nose-bleed (A turance tana nufin haɓo)
Haɗama - Tana nufi wawashe abu da yawa musamman idan ana haɗawa da rabon wasu.
Misali; Saboda haɗama ya kwashe abincin mutum uku shi kaɗai.
ENG; Greed (A turance tana nufin haɗama)
Haɗari - Tana nufin abin da zai iya cutarwa, ko tsautsayin da ke faruwa a kan titi.
Misali; 1. Shaƙar hayaƙin taba na da haɗari ga lafiya.
2. Ya samu karaya sakamakon haɗarin mota.
ENG; Risk, Accident (A turance tana nufin haɗari)
Haɗiye - Tana nufin cinyewa, ko shigar abu cikin ciki ta hanyar maƙogwaro.
Misali; Ya haɗiye alawar da na ba shi.
ENG; Swallow (A turance tana nufin haɗiye)
Kishiyarta; Amayar
Haƙa - Tana nufin yin rami.
Misali; An haƙa rijiya a bakin masallaci.
ENG; Dig (A turance tana nufin haƙa)
Kishiyarta; Binne
Haƙarkari - Tana nufin ɗaya daga cikin sassan jikin ɗan Adam, gefen hagu da daman ƙirji.
Misali; Sanyi ya sa min ciwon haƙarƙari.
ENG; Rib (A turance tana nufin haƙarƙari)
Haƙilo - Tana nufin yin abu da gaske ka'in da na'in, tare da kai komo.
Misali; Ɗaliban na ta haƙilo don ganin ba su faɗi jarrabawa ba.
ENG; Giving much effort for little gain (A turance tana nufin haƙilo)
Haƙori - Tana nufin ɗaya daga cikin sassan jikin ɗan Adam da sauran halittu, wanda ake amfani da shi wajen tauna.
Misali; Ba zai iya tauna ƙashi ba saboda ba shi da haƙori.
ENG: Tooth (A turance tana nufin haƙori)