Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Hauka - Tana nufin rashin ciwon rashin hankali ko gushewar hankali. Misali; Ya shekara goma yana fama da ciwon hauka. ENG; Madness (A turance tana nufin hauka) Kishiyarta; Hankali
Hauni - Tana nufin mai yanke hukuncin kisa. Misali; Ɓarayin sun gamu da hauni a kotu. ENG; Executioner (A turance tana nufin hauni)
Haure - Tana nufin haƙori. Misali; Da hauren giwa ake haɗa maganin. ENG; Tusk (A turance tana nufin haure)
Hausa person who has no Fulani ancestry - A turance tana nufin haɓe. Misali; Abokin Jauro haɓe ne. HAU;  Haɓe (Tana nufin wanda ba bafulatani ba. Fulani kan kira wanda ba ɗan ƙabilarsu ba da wannan suna)
Haushi - Tana nufin kukan kare. Misali; Tuna farkon dare kare yake ta haushi a waje. ENG; Barking (A turance tana nufin haushi)
Have as much as one can stand - A turance tana nufin ginsa. Misali; Cin abinci nau'i ɗaya kullum na da ginsa. HAU; Ginsa (Tana nufin isa ko fita daga rai)
Hawainiya - Tana nufin wata dabba mai kama da ƙadangare, tana canja launi ta saje da inda take don ba wa kanta kariya daga abokan gaba. Misali; Hawainiya na tafiya ne a hankali kamar dodon koɗi. ENG: Chameleon (A turance tana nufin hawainiya)
Hayaƙi - Tana nufin abin da yake fitowa daga wuta idan an kunna, yana cutar da huhu musamman idan ana shaƙar sa da yawa. Misali; Hayaƙi yana tashi saboda itacen ɗanye ne. ENG; Smoke (A turance tana nufin hayaƙi)
Haze - A turance tana nufin hazo. Misali; Yau an tashi da hazo. HAU; Hazo (Tana nufin ƙura da disashewar gari a lokacin sanyi)
Hazo - Tana nufin ƙura da disashewar gari a lokacin sanyi. Misali; Yau an tashi da hazo. ENG; Haze (A turance tana nufin hazo)
1 6 7 8 9 10 24