Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Harzuƙa - Tana nufin saurin fushi.
Misali; Ya harzuƙa da yawa shi yasa ya kai masa naushi.
ENG; Become Suddenly Angry (A turance tana nufin harzuƙa)
Hasara - Tana nufin rasa wani abu.
Misali; Sun yi hasara sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku a yankin su.
ENG; Misfortune/Loss (A turance tana nufin hasara)
Kishiyarta; Riba
Haske - Tana nufin abin da ke fitowa idan rana ta fito kuma yake gushewa idan ranar ta faɗi.
Misali; Haske ya mamaye ɗakin sakamakon kunna fitilar da Laure ta yi.
ENG; Light (A turance tana nufin haske)
Kishiyarta; Duhu
Hassada - Tana nufin jin ƙyashi ko baƙin ciki idan wani ya samu abin alkhairi ko cigaba ko ɗaukaka da sauransu.
Misali; Daga cikin munanan ɗabi'u akwai hassada da kuma ƙarya.
ENG; Envy (A turance tana nufin hassada)
Hasumiya - Tana nufin wani siririn gini mai tsawo da ake yi a masallaci ko majami'a.
Misali; An fara gyara fentin hasumiyar masallacin unguwar mu.
ENG; Tower (A turance tana nufin hasumiya)
Hatimi - Tana nufin wata shaida ko alama.
Misali; Wasiƙar tana ɗauke da hatimin sarki.
ENG; Seal (A turance tana nufin hatimi)
Hatsabibi - Tana nufin mutum mai ɗabi'un ban mamaki ko wanda yake abubuwan tsautsayin da ba kowa ne zai iya ba.
Misali; Jauro hatsabibi ne, jiya ya shiga dajin da ba kowa ne yake shiga ya fito lafiya ba.
ENG; Person with extra ordinary ability (A turance tana nufin hatsabibi)
Hatsaniya - Tana nufin cacar baki ko cece-kuce.
Misalil; Mata da mijin sun yi hatsaniya har ta kai matar ta yi yaji.
ENG; Loud Argument (A turance tana nufin hatsaniya)
Hatsi - Tana nufin tsabar abinci kamar gero, masara, dawa da sauransu.
Misali; Akwai rumbun hatsi a gidan maigari.
ENG; Grain (A turance tana nufin hatsi)
Haughtiness - A turance tana nufin izza.
Misali; Sarautar da aka naɗa shi ta sa shi jin izza.
HAU; Izza (Tana nufin jin isa da faɗin rai)