Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Haraji - Tana nufin kuɗin da al'umma ke biya ga shugabanni wanda ake amfani da su don aiwatar da ayyukan more rayuwa.
Misali; An tsaurara hukunci a kan masu ƙin biyan haraji a lardinmu.
ENG; Tax (A turance tana nufin haraji)
Haram - Tana nufin abin da Allah ya hana.
Misali; Shan giya haram ne a musulunci.
ENG; Any Unlawful Act (A turance tana nufin haram)
Kishiyarta; Halal
Harama - Tana nufin ƙudirin yin wani abu.
Misali; Na yi harama za ni masallaci don na ji kiran sallah.
ENG; Intending To (A turance tana nufin harama)
Harara - Tana nufin kallon raini ko wulaƙanci.
Misali; Harara ta yake don na dake shi.
ENG; Glare At (A trurance tana nufin harara)
Harawa - Tana nufin busasshen ganyen wake ko na gyaɗa da sauransu wanda ake ba wa dabbobi.
Misali; Dabbobin na cinye buhun harawa biyu a mako guda.
ENG; Leaves or stalk of beans, groundnut etc (A turance tana nufin harawa)
Hargitsi - Tana nufin rashin daidaito.
Misali; An samu hargitsi a tsakanin maƙotan guda biyu.
ENG; Disagreement (A turance tana nufin hargitsi)
Harka - Tana nufin al'amura musamman na kasuwanci.
Misali; Aboki na ya kawo min harka ta arziƙi.
ENG; Business/Affair (A turance tana nufin harka)
Harlot - A turance tana nufin karuwa.
Misali; Kowa ya san tsohuwar kilaki ce, sai dai mu ce Allah ya shirye mu duka.
HAU; Karuwa (Tana nufin (karuwa) mace mai zaman kanta)
Harsashi - Tana nufin tushe.
Misali; An dasa harsashin gina makarantar islamiyya a yankin mu.
ENG; Foundation (A turance tana nufin harsashi)
Harshe - Tana nufin gaɓar da ake magana da ita wadda take cikin baki.
Misali; Ya tauna harshe yayin da yake cin abinci.
ENG; Tongue (A turance tana nufin harshe)