Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Hana - Tana nufin ƙin ba da dama.
Misali; An hana zuwa makaranta a makare.
ENG; Prevent (A turance tana nufin hana)
Hanci - Tana nufin gaɓar da ake numfashi wadda take a saman baki.
Misali; Ƙurji ya fito mata a saman hanci mai ɗan karen ciwo.
ENG; Nose (A turance tana nufin hanci)
Hand - A turance tana nufin hannu.
Misali; Na wanke hannu zan ci abinci.
HAU; Hannu (Tana nufin gaɓa daga cikin gaɓɓan jiki)
Handball Federation of Nigeria (HFN) - Hukumar Ƙwallon Hannu Ta Najeriya
Handkerchief - A turance tana nufin hankici.
Misali; Na goge fuska ta da hankici don na yi gumi da yawa.
HAU; Hankici (Tana nufin ƙyallen da ake goge gumi)
Hanga - Tana nufin gano abu daga nesa.
Misali; Kamar Talatu na hanga tana shiga gidan maigari.
ENG; See something from afar (A turance tana nufin hanga)
Hangum - Tana nufin ciwon da ke kumbura gefen kunci zuwa kunne.
Misali; Hangum ne ya fitowa Safiya, tana kan shan magani.
ENG; Mumps (A turance tana nufin hangum)
Haniniya - Tana nufin kukan doki.
Misali; Dokunan suna ta haniniya tun safe.
ENG; Neighing (A turance tana nufin haniniya)
Hankaka - Tana nufin tsuntsu mai launi biyu, ƙirjinsa fari sauran jikinsa baƙi.
Misali; Ya kamo hankaka da ya fita farauta.
ENG; Pied Crow (A turance tana nufin hankaka)
Hankali - Tana nufin sanin ya kamata.
Misali; Idris yana da hankali da sanin ya kamata.
ENG; Sense (A turance tana nufin hankali)
Kishiyarta: Rashin Hankali