Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Hali - Tana nufin ɗabi'a.
Misali; Ya kasance mai kyakkyawan hali shi yasa ake son shi.
ENG; Character (A turance tana nufin hali)
Halitta - Tana nufin ƙirƙirarren abu.
Misali; Allah shi ne ya ƙagi Annabi Muhammad (SAW) ya sa ya zamo shugaban halitta baki ɗaya.
ENG; Creature (A turance tana nufin halitta)
Hallara - Tana nufin zuwa ko bayyana ko samun damar halarta.
Misali; Mutane sun hallara, ya kamata a fara taron.
ENG; Appear/Arrive (A turance tana nufin hallara)
Hamada - Tana nufin guri mai cike da rairayi da duwatsu wanda dabbobi da tsirrai ba sa sakewa.
Misali; Ƙasar da ke maƙotaka da mu cike take da hamada
ENG; Desert (A turance tana nufin hamada)
Hamayya - Tana nufin kishi ko takun saƙa.
Misali; Abokan hamayya ne su a siyasa shi yasa ba sa ga maciji.
ENG; Rivalry/Opponent (A turance tana nufin hamayya)
Hambuɗa - Tana nufin ɗiban abu a watsa a baki.
Misali; Madara ta hambuɗa a baki ta gudu.
ENG; Throw powdered or ground thing into the mouth (A turance tana nufin hambuɗa)
Hamma - Tana nufin fitar da iska ta hanyar buɗe baki wanda jin yunwa ko bacci ke sa wa.
Misali; Tun ɗazu nake hamma saboda yunwa nake ji matuƙa.
ENG; Yawning (A turance tana nufin hamma)
Hammata - Tana nufin gaɓar ƙarƙashin hannu.
MIsali; An ce goga alimun a hammata yana hana warin jiki.
ENG; Armpit (A turance tana nufin hammata)
Hammer - A turance tana nufin guduma.
Misali; Ya buge hannu da guduma a lokacin da yake gyaran kujerar.
HAU; Guduma (Tana nufin abin da ake amfani da shi wajen buga katako ko ƙusa da sauransu)
Hamsin - Tana nufin goma sau biyar.
Misali; Bulalar da aka yi masa ta kai hamsin.
ENG; Fifty (A turance tana nufin hamsin)