Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Herd/Flock - A turance tana nufin garke.
Misali; Yana da shanu garke guda.
HAU; Garke (Tana nufin dabbobi da yawa, kamar akuyoyi, shanu da sauransu)
Hide - A turance tana nufin ɓoye.
Misali; Yaran sun ɓoye kayan wasan su, mun nema mun rasa.
HAU; Ɓoye (Tana nufin a ɗauke abu a kai shi inda ba za a ganshi ba)
High Way - A turance tana nufin karauka.
Misali; Bin karauka sai manyan direbobi.
HAU; Karauka (Tana nufin babbar hanya ko babban titin da ke sa-da jihohi)
Hikima - Tana nufin dabara ko baiwa.
Misali; Ya yi amfani da hikima wajen daidaita abokan da suka samu saɓani.
ENG; Wisdom (A turance tana nufin hikima)
Hippopotamus - A turance tana nufin dorina.
Misali; Akwai dorina a gidan ajiye namun dajin garinmu.
HAU; Dorina (Tana nufin wata babbar dabba da ke rayuwa a ruwa da kuma doron ƙasa)
Hisabi - Tana nufin lissafa ayyukan mutum masu kyau da marasa kyau a ranar lahira.
Misali; Muna fatan samun dace a ranar hisabi.
ENG; Reckoning up the good and bad deeds of a person on judgement day (A turance tana nufin hisabi)
Historical Society of Nigeria (HSN) - Ƙungiyar Malaman Tarihi Ta Najeriya
Hoda - Tana nufin gari mai laushi da mata ke shafawa a fuska don yin ado, akwai ja akwai fara da sauransu.
Misali; An zubo hoda kala-kala a kayan lefen Tsahare.
ENG; Powder (A turance tana nufin hoda)
Hoe - A turance tana nufin fartanya.
Misali; Ado ya saɓa fartanya ya nufi gona.
HAU; Fartanya (Tana nufin wani ƙarfe mai ƙota da ake amfani da shi don yin noma)
Hole - Tana nufin hutu da jin daɗi.
Misali; Yau za mu hole mu sha shagali saboda an ɗaura auren ƙawarmu.
ENG; Relax, Enjoy (A turance tana nufin hole)