Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Haƙuri - Tana nufin dangana da rashin ɗaukar mataki idan an maka laifi.
Misali; Ya samu mace mai haƙuri shi yasa zamansu ya yi tsayi.
ENG; Patience (A turance tana nufin haƙuri)
Kishiyarta; Rashin haƙuri
He-goat - A turance tana nufin bunsuru.
Misali; Malam Rabi'u ya siyo bunsuru shekaran jiya.
Kishiyarta; Akuya
HAU; Bunsuru (Tana nufin namijin akuya.)
Head Pad - A turance tana nufin gammo.
Misali; Ka sa gammo a kanka saboda kayan na da nauyi.
HAU; Gammo (Tana nufin tsumman da ake nannaɗawa a sa a saman kai idan za a ɗauki kaya)
Head-tie - A turance yana nufin maɗaurin kai na mata.
Misali; Kande ta ɗaure kai da adiko.
HAU; Adiko (Maɗaurin kai na mata)
Heads - A turance tana nufin kawuna.
Misali; 'Yan gidan manyan kawuna garesu.
HAU; Kawuna (Tana nufin jam'in kai)
Heads of State & Government of the Niger Basin Authority - Kadaurar Shugabannin Ƙasashe da Gwanmnatoci Mamallakar Kogin Kwara
Help - A turance tana nufin gudunmawa.
Misali; Gwamnati ta kawo gudunmawa ga waɗanda ibtila'in gobara ya afkawa.
HAU; Gudunmawa (Tana nufin tallafi ko agaji)
Help/Assistance - A turance yana nufin taimako.
Misali; Gwamnati ta kai agaji gidan gyaran hali da tarbiyya.
HAU; Agaji (Yana nufin taimako)
Hen/Chicken - A turance tana nufin kaza.
Misali; Idan aka yi girki da kaza, ɗanɗanon na musamman ne.
HAU; Kaza (Tana nufin ɗaya daga cikin dabbobin gida)
Herb used in making soup - A turance tana nufin karkashi.
Misali; Tuwo zan dafa da miyar karkashi yau.
HAU; Karkashi (Tana nufin ganyen da ake miya da shi, yana da yauƙi sosai)