Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Father - A turance tana nufin mahaifi. Misali; Baba yana da jikoki arba'in a yanzu. HAU; Baba (Tana nufin mahaifi)
Fatsa - Tana nufin abin kama kifi. Misali; Ya ɗauki fatsa ya nufi kogi zai yi su. ENG; Fish-hook (A turance tana nufin fatsa)
Fawa - Tana nufin sana'ar siyar da nama. Misali; Wanda zai aure ta fawa yake. ENG; Butchering (A turance tana nufin fawa)
Fayyace - Tana nufin yin cikakken bayani. Misali; Malamin ya fayyace mana darasin dalla-dalla. ENG; Explain Thoroughly (A turance tana nufin fayyace)
Faɗa - Tana nufin ɗaga murya da faɗin maganaganu marasa daɗi saboda ɓacin rai. Misali; Ɗaliban faɗa suke bayan an tashi daga makaranta. ENG; Quarrel (A turance tana nufin faɗa)
Faƙiri - Tana nufin talaka wanda ba shi da komai. Misali; Idan za ka yi sadaka ka nemi faƙiri ka ba shi. ENG; Poor, Destitute (A turance tana nufin faƙiri)
February - A turance yana nufin wata na biyu a shekara.  Misali; Za a gudanar da taron a watan Fabrairun wannan shekarar. HAU; Fabrairu (Wata ne na biyu a shekara)
Feda - Tana nufin inda ake sa ƙafa a tuƙa keke. Misali; Keken na da matsalar feda sai an gyara. ENG; Bicycle Pedal (A turance tana nufin feda)
Federal Capital Territory Administration (FCTA) - Ma'aikatar Birnin Tarayya
Federal Character Commission (FCC) - Hukumar  Raba-Daidai Ta kasa
1 5 6 7 8 9 18