Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Fasahar Sana’a - Dabarar sarrafa tunani wajen aiwatar da aikin ko sana'o'in hannu.
Fassara - Tana nufin daga wani harshe zuwa wani harshe. Misali; Ya fassara littafin daga harshen larabci zuwa harshen Hausa. ENG; Translation (A turance tana nufin fassara)  
Fasting - A turance yana nufin azumi.  Misali; Ranar litinin zan yi azumi idan Allah ya kai mu. HAU; Azumi (Yana nufin barin ci da sha da mu'amalar auratayya tun daga fitowar alfijir har zuwa faɗuwar rana)
Fasto - Tana nufin limamin coci. Misali; Maƙococinsa babban fasto ne. ENG; Pastor (A turance tana nufin fasto)
Fat - A turance tana nufin ɓulele. Misali; Sabon ɗalibin da aka kawo mana ɓulele ne. HAU; Ɓulele (Tana nufin mai ƙiba)
Fat On Meat - A turance tana nufin kitse. Misali; Ragon yana da kitse ainun, maiƙon jikinsa ya isa a soya shi. HAU; Kitse (Tana nufin maiƙon da ke jikin nama)
Fata - Tana nufin abin da ya lulluɓe jikin mutum ko dabba. Misali; Ana amfani da fata don yin jakunkuna da takalma. ENG; Skin (A turance tana nufin fata)
Fatali - Tana nufin watsi da abu. Misali; Alƙali ya yi fatali da hujjojin da aka bayar. ENG; Disregard (A turance tana nufin fatali)
Fatalwa - Tana nufin wanda ya mutu ya dinga gizo. Misali; An ce fatalwar Idi tana fitowa da daddare. ENG; Ghost (A turance tana nufin fatalwa)
Fatara - Tana nufin rashin kuɗi ko abin duniya. Misali; Gidan suna fatarar abinci. ENG; Lack (A turance tana nufin fatara)
1 4 5 6 7 8 19