Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Forge - A turance tana nufin ƙera.
Misali: Maƙeri yana ƙera fartanya, wuƙa, da sauran kayayyakin noma.
HAU: Ƙera (Tana nufin aikin sarrafa ƙarfe ko ƙirƙirar kayan aiki ta hanyar amfani da wuta da guduma)
Forum - Ƙungiya, Kadaura
Foundation - Gidauniya
Foundation - A turance tana nufin harsashi.
Misali; An dasa harsashin gina makarantar islamiyya a yankin mu.
HAU; Harsashi (Tana nufin tushe)
Four - A turance tana nufin huɗu.
Misali; Musulunci ya ba wa maza damar auren mata guda huɗu.
HAU; Huɗu (Tana nufin lambar da ke bin bayan uku)
Fragrant - A turance tana nufin ƙamshi.
Misali; Furen nan yana da ƙamshi mai daɗi.
HAU; Ƙamshi (Tana nufin shaƙar daddaɗar iska)
Friday - A turance tana nufin rana ta biyar a mako.
Misali; Yara na ɗokin zuwa masallaci ranar Juma'a.
HAU; Juma'a (Rana ce ta biyar a ranakun mako)
Fried cake made of wheat flour - A turance tana nufin fanke.
Misali; An yi sadakar fanke a gidan mutuwar.
HAU; Fanke (Tana nufin nau'in abin ci da ake yi da fulawa da sikari da mai da sauransu)
Fried Groundnut Balls - A turance tana nufin ƙuli-ƙuli.
Misali: Yara suna son cin ƙuli-ƙuli tare da koko da safe.
HAU: Ƙuli-ƙuli (Tana nufin wani nau’in abin ci da ake yi daga gyadar da aka matse man ta, sannan a soya ta har ta yi ƙarfi da ɗan ƙamshi)
Frog - A turance tana nufin kwaɗo.
Misali; Tahir ya ga kwaɗo a bakin kwatar da ke ƙofar gidansu.
HAU; Kwaɗo (Tana nufin wata dabba da ke rayuwa a ruwa kuma da doron ƙasa)