Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Foundation - Gidauniya
Foundation - A turance tana nufin harsashi. Misali; An dasa harsashin gina makarantar islamiyya a yankin mu. HAU; Harsashi (Tana nufin tushe)
Four - A turance tana nufin huɗu. Misali; Musulunci ya ba wa maza damar auren mata guda huɗu. HAU; Huɗu (Tana nufin lambar da ke bin bayan uku)
Friday - A turance tana nufin rana ta biyar a mako.  Misali; Yara na ɗokin zuwa masallaci ranar Juma'a. HAU; Juma'a (Rana ce ta biyar a ranakun mako)
Fried cake made of wheat flour - A turance tana nufin fanke. Misali; An yi sadakar fanke a gidan mutuwar. HAU; Fanke (Tana nufin nau'in abin ci da ake yi da fulawa da sikari da mai da sauransu)
Frog - A turance tana nufin kwaɗo. Misali; Tahir ya ga kwaɗo a bakin kwatar da ke ƙofar gidansu. HAU; Kwaɗo (Tana nufin wata dabba da ke rayuwa a ruwa kuma da doron ƙasa)
Fronds of Dum-palm - A turance tana nufin kaba. Misali; Tabarmar da muke zaune ta kaba ce. HAU; Kaba (Tana nufin ganyen bishiyar goruba da ake amafani da shi wajen yin tabarma da mafici da sauransu)
Fruitless Search - A turance tana nufin bilimbituwa. Misali; Mafarautan bilimbituwa kawai za su yi a dajin saboda babu namun daji yanzu. HAU; Bilimbituwa (Tana nufin neman abu a rasa a yi ta bulayi, ko kuma neman da babu sakamako)
Fulfilment Of Wish - A turance tana nufin ijaba. Misali; Allah ya yi mana ijaba, yau ruwa ya sauka. HAU; Ijaba (Tana nufin cikar buri)
Full stop - A turance tana nufin aya.  Misali; Aya alama ce da ke nuna jimla ta zo ƙarshe. HAU; Aya (Alama ce ta dakatawa a cikin rubutu)
1 14 15 16 17 18