Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Fitsari - Tana nufin wani ruwa da jiki ba ya buƙata wanda ke fitowa daga ƙoda.
Misali; Amir ya yi fitsari a jikinsa.
ENG; Urine (A turance tana nufin fitsari)
Fixed Punishment for transgressing islamic law - A turance tana nufin haddi.
Misali; Haddin sata yanke hannu ne a musulunci.
HAU; Haddi (Tana nufin hukuncin da ake wa wanda ya aikata laifi a musulunci)
Fiyayye - Tana nufin wanda ya ɗara kowa. (Annabi Muhammad S.A.w)
Misali; Manzon Allah S.A.W shi ne fiyayyen halitta.
ENG; Superior Person (A turance tana nufin fiyayye)
Fiƙa - Tana nufin haƙoran gaba.
Misali; Yaron ya fara fiƙa.
ENG; Canine Tooth (A turance tana nufin fiƙa)
Flea - A turance tana nufin ƙuma.
Misali: Karen ya kamu da ƙuma, shi ya sa yake ta susa kullum.
HAU: Ƙuma (Tana nufin wani ƙaramin ƙwaro mai tsalle wanda ke rayuwa a jikin dabbobi ko mutane, yana tsotsar jini kuma yana iya haddasa ƙaiƙayi)
Flirting - A turance tana nufin Kwarkwasa.
Misali: Sani yace budurwarsa na yawan yi masa kwarkwasa a lokacin da ya je hira.
HAU; Kwarkwasa (Tana nufin jan hankali ta hanyar magana ko juya sassan jiki)
Flood - A turance tana nufin ambaliya.
Misali; An yi ambaliyar ruwa a jihar Borno a shekarar 2024.
HAU; Ambaliya (Tana nufin ɓarkewar ruwa daga inda yake a tsare ko kuma yawaitar ruwan sama har ta kai ga ya yi ɓarna)
Flour - A turance tana nufin gari.
Misali; Mun siyo niƙaƙƙiyar masara za mu yi tuwo.
HAU; Gari (Tana nufin niƙaƙken abu)
Flower - A turance tana nufin fure.
Misali; An tsinko fure daga lambu.
HAU; Fure (Tana nufin tsiro mai ban sha'awa mai ɗauke da launi daban-daban)
Fly - A turance tana nufin ƙuda.
Misali: Ƙuda na yawan taruwa a kan abincin da aka bari a buɗe.
HAU: Ƙuda (Tana nufin ƙaramin ƙwaro mai tashi wanda ake yawan samu a kusa da abinci ko ƙazanta)