Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Fishing Net - A turance tana nufin koma.
Misali; Akwai koma a cikin jakar da yake tafiya SU da ita.
HAU; Koma (Tana nufin abin da masunta suke amfani da shi wajen kama kifi)
Fitacce - Tana nufin wanda ya shahara.
Misali; Alh. Sule fitacce ne a unguwar.
ENG; Famous (A turance tana nufin fitacce)
Fito - Tana nufin fitar da iska da baki har ya ba da wata siririyar ƙara.
Misali; Waye yake fito a waje?
ENG; Whistling (A turance tana nufin fito)
Fitsari - Tana nufin wani ruwa da jiki ba ya buƙata wanda ke fitowa daga ƙoda.
Misali; Amir ya yi fitsari a jikinsa.
ENG; Urine (A turance tana nufin fitsari)
Fixed Punishment for transgressing islamic law - A turance tana nufin haddi.
Misali; Haddin sata yanke hannu ne a musulunci.
HAU; Haddi (Tana nufin hukuncin da ake wa wanda ya aikata laifi a musulunci)
Fiyayye - Tana nufin wanda ya ɗara kowa. (Annabi Muhammad S.A.w)
Misali; Manzon Allah S.A.W shi ne fiyayyen halitta.
ENG; Superior Person (A turance tana nufin fiyayye)
Fiƙa - Tana nufin haƙoran gaba.
Misali; Yaron ya fara fiƙa.
ENG; Canine Tooth (A turance tana nufin fiƙa)
Flood - A turance tana nufin ambaliya.
Misali; An yi ambaliyar ruwa a jihar Borno a shekarar 2024.
HAU; Ambaliya (Tana nufin ɓarkewar ruwa daga inda yake a tsare ko kuma yawaitar ruwan sama har ta kai ga ya yi ɓarna)
Flour - A turance tana nufin gari.
Misali; Mun siyo niƙaƙƙiyar masara za mu yi tuwo.
HAU; Gari (Tana nufin niƙaƙken abu)
Flower - A turance tana nufin fure.
Misali; An tsinko fure daga lambu.
HAU; Fure (Tana nufin tsiro mai ban sha'awa mai ɗauke da launi daban-daban)