Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Financil Reporting Council of Nigeria (FRCN) - Hukumar Rawaito Hada-hadar Kuɗi Ta Najeriya
Fincika - Tana nufin jan abu da ƙarfi.
Misali; Ta tsinka jakar da ta fincika.
ENG; Pull out suddenly with force (A turance tana nufin fincika)
Find Fault - A turance tana nufin kushe.
Misali; Duk yanda abu ya kai da kyau mahassada sai sun kushe shi.
HAU; Kushe (Tana nufin faɗar aibu ko ƙaƙalo laifin abu)
Fingernail - A turance yana nufin farce.
Misali; Na kira mai yankan akaifa zai yanke min yanzu.
HAU; Farce (Yana nufin farce, na yatsun hannu ko ƙafa)
Fingernail - A turance tana nufin farce.
Misali; Salihu yana sana'ar yankan farce.
HAU; Farce (Tana nufin ƙumba)
Firamare - Tana nufin matakin farko na karatun boko.
Misali; Farida ta shiga firamare.
ENG; Primary School (A turance tana nufin firamare)
First Prayer - A turance tana nufin sallar farko a rana.
Misali; Na samu sallar asuba a jam'i.
HAU; Asuba (Salla ce ta farko a rana)
Fiscal Responsibility Commission (FRC) - Hukumar Alkinta kuɗaɗen Haraji
Fish - A turance tana nufin kifi.
Misali; San'ar kifi sana'a ce mai albarka.
HAU; Kifi (Tana nufin ɗaya daga cikin dabbobin ruwa)
Fish-hook - A turance tana nufin fatsa.
Misali; Ya ɗauki fatsa ya nufi kogi zai yi su.
HAU; Fatsa (Tana nufin abin kama kifi)