Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Female Slave - A turance tana nufin kuyanga.
Misali; Mallakar kuyanga sai masu hannu da shuni.
HAU; Kuyanga (Tana nufin baiwa mace)
Fensir - Tana nufin abin rubutu.
Misali; 'Yan aji ɗaya da fensir suke rubutu.
ENG; Pencil (A turance tana nufin fensir)
Fetur - Tana nufin man da ake zubawa a mota ko wani abin hawa don ya yi tafiya.
Misali; Fetur ya yi matuƙar tsada a Najeriya.
ENG; Petrol (A turance tana nufin fetur)
Few - A trurance tana nufin kaɗan.
Misali; Sun yi aiki mai yawa amma ya ba su kuɗi kaɗan.
HAU; Kaɗan (Tana nufin babu yawa)`
Kishiyarta; Da yawa
Feƙe - Tana nufin saka abu ya yi kaifi.
Misali; An feƙe wuƙaƙen kafin a yanka naman.
ENG; Sharpen (A turance tana nufin feƙe)
Fifth month of Islamic calendar - A turance tana nufin jimada awwal.
Misali; A watan Jimada Awwal za a yaye ɗaliban.
ENG; Jimada Awwal (Tana nufin wata na biyar a watannin musulunci)
Fifty - A turance tana nufin hamsin.
Misali; Bulalar da aka yi masa ta kai hamsin.
HAU; Hamsin (Tana nufin goma sau biyar)
Fige - Tana nufin cire gashi.
Misali; Na biya kuɗi an fige min kajin da na siya.
ENG; Pluck (hair, feathers)(A turance tana nufin fige)
Filla-filla - Tana nufin daki-daki.
Misali; Ya yi mana bayani filla-filla.
ENG; Step by step (A turance tana nufin filla-filla)
Financial Market Dealers Association (FMDA) - Ƙungiyar Dillalan Hada-hadar Kuɗi Ta Najeriya