Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Certified Institute of Cost Management of Nigeria (CICMA) - cibiyar naƙaltar kididdigar uwar kuɗi ta najeriya
Certified Pension institu of Warehousing Materials Management (CPIWMM) - cibiyar naƙaltar dabarun ajiyar kayayyaki
Certified Pension Institute of Nigeria (CPIN) - cibiyar naƙaltar Harkokin fansho ta najeriya
Chain - A turance tana nufin kaca. Misali; An canjawa keken kaca, yanzu yana tafiya lafiya lau. HAU; Kaca (Tana nufin sarƙa musamman irin wadda ke juya kafar keke)
Chair - A turance tana nufin kujera. Misali; Inna ta siyo sabuwar kujera. HAU; Kujera (Tana nufin abin da ake zama a kai)  
Chameleon - A turance tana nufin hawainiya. Misali; Hawainiya na tafiya ne a hankali kamar dodon koɗi. HAU: Hawainiya (Tana nufin wata dabba mai kama da ƙadangare, tana canja launi ta saje da inda take don ba wa kanta kariya daga abokan gaba.)
Chana Radio International (CRI) - Gidan Rediyon Caina/Sin
Change - A turance tana nufin canja. Misali; An canja lokacin jarrabawar daga ƙarfe ɗaya zuwa ƙarfe biyu na rana. HAU; Canja (Tana nufin sake wani abu da wani)
Change of position - A turance tana nufin juyi. Misali; Indo ta zata naƙuda ta fara amma juyi ne. HAU; Juyi (Tana nufin canjawa daga wani yanayi zuwa wani)
Character - A turance tana nufin hali. Misali; Ya kasance mai kyakkyawan hali shi yasa ake son shi. HAU; Hali (Tana nufin ɗabi'a)
1 5 6 7 8 9 34