Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Carabke - Tana nufin wasa da ake yi da dutse, inda ake wurga dutse sama a cafe shi da hannu. Misali; 'Yan matan suna 'yar carabke a ƙofar gida. ENG; Game of tossing and catching stones on hands (A turance tana nufin carabke)
Caring For - A turance tana nufin gata. Misali; 'Ya'yan Alhaji Jibrin na da gata saboda ya sa su a makaranta mai tsada. HAU; Gata (Tana nufin samun duk abinda ake buƙata na rayuwa)
Carkwai - Tana nufin zaƙi sosai. Misali; Raken yana da zaƙi carkwai. ENG; Very Sweet (A turance tana nufin carkwai)
Carrying load for payment - A turance tana nufin dako. Misali; Ƙungiyar masu dako sun koka kan ƙarancin biyansu da mutane ke yi. HAU; Dako (Tana nufin ɗaukarwa mutum kaya a kai masa inda yake so, ya biya)
Cartilage - A turance tana nufin guringuntsi. Misali; Guringuntsi na da daɗi musamman a miyar taushe. HAU; Guringuntsi (Tana nufin ƙashi mai laushi da ke jikin ɗan Adam da dabba)
Casa - Tana nufin cire tsaba daga cikin kwansonta, kamar shinkafa da gero da sauransu. Misali; Sai an casa shinkafar sannan za a dafa. ENG; Thresh Grain (A turance tana nufin casa)
Cassava Flour - A turance tana nufin kwaki. Misali; Ɗaliban makarantun kwana suna son kwaki sosai HAU; Kwaki (Tana nufin garin rogo)
Cat - A turance tana nufin mage. Misali; Gidansu Hanan suna da ƙaton kule. HAU; Kule (Tana nufin mage)
Cat -

A turance tana nufin kyanwa.

Misali: Kyanwar gidanmu tana kama ɓeraye.

HAU: Cat (Tana nufin dabba mai kama da damisa ƙarama wadda ake kiwo a gida).

Catch - A turance tana nufin kama. Misali; Jami'an tsaro sun kama masu lefi da yawa a wannan makon. HAU; Kama (Tana nufin riƙe abu da hannu)
1 2 3 4 5 6 37