Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Cripple - A turance tana nufin gurgu. Misali; Ya zama gurgu ne sanadiyyar hatsarin motar da suka yi. HAU; Gurgu (Tana nufin wanda ba shi da ƙafa) Kishiyarta; Mai ƙafa
Crocodile - A turance tana nufin kada. Misali; Ruwan sama mai yawa ya sa kada ta fito daga gidan ajiyar namun daji. ENG; Kada (Tana nufin wata dabbamai kaushin baya kuma mai siffar ƙadangare da ke rayuwa a ruwa, amma tana da girma ainun)
Cross In Front - A turance tana nufin gifta. Misali; Na ga Iliya ya gifta ɗazu. HAU: Gifta (Tana nufin wucewa ta gaban abu)
Crown - A turance tana nufin kambi.  Misali; Sarkin yana sanye da kambi a lokacin da aka yi taron. HAU; Kambi (Tana nufin wani abu mai kamar hula da sarakuna da 'ya'yansu ke sa wa)
Crownbird - A turance tana nufin gauraka. Misali; Ana samun tsuntsun gauraka a kudu maso yammacin Afirika. HAU; Gauraka (Tana nufin tsuntsu wanda yake rayuwa kusa da fadamu)
Crumbs - A turance tana nufin burbuɗi. Misali; Ta yi amfani da burbuɗin biredi wajen suyar dankalin. HAU; Burbuɗi (Tana nufin abin da ya marmashe ya zama gari)
Crush - A turance tana nufin dagargaza. Misali; Matasan sun dagargaza gilasan ginin yayin faɗace-faɗacensu. HAU; Dagargaza (Tana nufin farfasa abu a yi masa rugu-rugu)
Crying - A turance tana nufin kuka. Misali; Safiya ta sha kuka lokacin da mahaifinta ya rasu. HAU; Kuka (Tana nufin zubar hawaye daga idanu sakamakon murna ko ɓacin rai)
Cudgel - A turance tana nufin kulki. Misali; Ɗan dokar na riƙe da kulki lokacin da suka je kama ɓarayin. HAU; Kulki (Tana nufin gajeren sanda mai kauri wanda 'yan doka suke riƙewa)
Cuku-cuku - Tana nufin yin 'yan dabaru don samun abin da ake so. Misali; Ya yi cuku-cuku har ya samun aikin. ENG; Obtaining things through devious (A turance tana nufin cuku-cuku)
1 31 32 33 34