Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Consumer Protection Council (CPC) - Hukumar kare Haƙƙin matsayi (Mamori)
Contain - A turance tana nufin ƙunsa.
Misali: Wannan littafin tarihin Hausawa ya ƙunsa.
HAU: Ƙunsa (Tana nufin kasancewar wani abu a cikin wani abu)
Contract -
A turance tana nufin kwangila.
Misali; Kamfanin ya samu kwangila domin gina sabon asibiti.
HAU; Kwangila (Tana nufin yarjejeniya tsakanin ɓangarori biyu ko fiye domin gudanar da wani aiki ko ciniki)
Controversy - A turance tana nufin jayayya.
Misali; Tun safe suke jayayya a kan kuɗi.
HAU; Jayayya (Tana nufin faɗi in faɗa)
Cook - A turance tana nufin dafa
Misali; Sai da aka dafa abincin aka yi sadakar da shi.
HAU; Dafa (Tana nufin sa abu a cikin tukunya a zuba ruwa a ɗora a wuta har ya yi laushi)
Cook - A turance tana nufin kuku.
Misali; Gidan attajirai ne ake ajiye kuku.
HAU; Cook (Tana nufin wanda yake aikin dafa abinci)
Cool Off - A turance tana nufin huce.
Misali; Abincin da na kawo har ya huce kuna hira.
HAU; Huce (Tana nufin yin sanyi)
Copy Something Written - A turance tana nufin juya.
Misali; Idan kin gama rubutun ki ba ni na juya.
HAU; Juya (Tana nufin rubuta abu kamar yanda yake)
Copyright Society of Nigeria (CSN) - Ƙungiyar haƙƙin mallaka ta Nijeriya
Corner - A turance tana nufin kusurwa.
Misali; Na ajiye adakar a kusurwar ɗakin da muke kwana.
HAU; Kusurwa (Tana nufin kwana)