Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Cornstalk Fence - A turance tana nufin danga.
Misali; Baba yana waje jikin danga tare da amininsa suna magana.
HAU; Danga (Tana nufin kewaye gida da karan masara)
Corporation - Kamfani, Hukuma
Corps - Runduna, Hukuma
Corpse - A turance tana nufin gawa.
Misali; Duk wanda ya shiga yankin da ake yaƙi ya zama gawa.
HAU; Gawa (Tana nufi mataccen abu ko abinda ba shi da rai)
Correctly - A turance tana nufin dai-dai.
Misali; Wanda ya yi aikinsa dai-dai zai samu sakamako da kyautatawa.
HAU; Dai-dai (Tana nufin yadda ya dace)
Cotton - A turance tana nufin auduga.
Misali; Akwai gonakin auduga da yawa a garinmu.
HAU; Auduga (Tana nufin tsiro da ake shukawa a gona, ana amfani da ita wajen yin zare da tufafi da sauransu)
Cotton cap with pointed flaps which covers ears worn especially by fulani - A turance tana nufin haɓar kada.
Misali; Samarin sun yi kwalliyar haɓar kada
HAU; Haɓar Kada (Tana nufin hular gargajiya mai rufe kunnuwa wadda musamman fulani ke amfani da ita)
Council - Hukuma, Majalisa
Council for the Regulation of Engineering in Nigeria (CREN) - Hukumar inganta ayyukan injiniyoyi ta Najeriya
Council of Afracan Political Parties (CAPP) - Majalisar jam'iyyun siyasar Afirka