Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Cook - A turance tana nufin kuku. Misali; Gidan attajirai ne ake ajiye kuku. HAU; Cook (Tana nufin wanda yake aikin dafa abinci)
Cool Off - A turance tana nufin huce. Misali; Abincin da na kawo har ya huce kuna hira. HAU; Huce (Tana nufin yin sanyi)
Copy Something Written - A turance tana nufin juya. Misali; Idan kin gama rubutun ki ba ni na juya. HAU; Juya (Tana nufin rubuta abu kamar yanda yake)
Copyright Society of Nigeria (CSN) - Ƙungiyar haƙƙin mallaka ta Nijeriya
Corner - A turance tana nufin kusurwa. Misali; Na ajiye adakar a kusurwar ɗakin da muke kwana. HAU; Kusurwa (Tana nufin kwana)
Cornstalk Fence - A turance tana nufin danga. Misali; Baba yana waje jikin danga tare da amininsa suna magana. HAU; Danga (Tana nufin kewaye gida da karan masara)
Corporation - Kamfani, Hukuma
Corps - Runduna, Hukuma
Corpse - A turance tana nufin gawa. Misali; Duk wanda ya shiga yankin da ake yaƙi ya zama gawa. HAU; Gawa (Tana nufi mataccen abu ko abinda ba shi da rai)
Correctly - A turance tana nufin dai-dai. Misali; Wanda ya yi aikinsa dai-dai zai samu sakamako da kyautatawa. HAU; Dai-dai (Tana nufin yadda ya dace)
1 28 29 30 31 32 34