Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Compensation payable for accidental homicide or injury - A turance tana nufin diyya. Misali; Direban ya biya diyyar wanda ya mutu sakamakon haɗarin da ya faru. HAU: Diyya (Tana nufin kuɗin da ake biya sakamakon yin kisan kai ko ganganci)
Competition - A turance tana nufin gasa.  Misali; An sa gasa tsakanin 'yan aji biyu da 'yan aji uku. HAU; Gasa (Tana nufin gwaji ko auna tsakanin abubuwa guda biyu don fitar da wanda ya fi)
Complaining - A turance tana nufin gunaguni. Misali; Habu yana ta gunaguni saboda Shamsu ya dake shi. HAU; Gunaguni (Tana nufin yin ƙorafi ko magana ƙasa-ƙasa ba tare wanda ake yi don shi ya fahimci abinda ake faɗa ba)  
Complete - A turance tana nufin kammala. Misali; Idan kun kammala aikin da na ba ku sai ku tafi gida. HAU; Kammala (Tana nufin gamawa) Kishiyarta; Fara/Farawa
Completely - A turance tana nufin kaf. Misali; Ta kwashe kayanta kaf daga gidan, kun ga kenan ba ta niyyar dawowa. HAU; Kaf (Tana nufi duka ko gaba ɗaya)
Completely Gone - A turance tana nufin cancak. Misali; Ta ɗauke jakar cancak daga kan teburin. HAU; Cancak (Tana nufin ɗungurungum, wato a ɗauke abu gaba ɗayansa)
Computer Professionals Registration Council of Nigeria (CPRCN) - Hukumar ayyukan masana kwamfuta ta Najeriya
Confederation - Kadaura, Ƙungiya
Confederation of African Football (CAF) - Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka
Confused/Flustered - A turance tana nufin kiɗime. Misali; Duk sun kiɗime saboda tashin hankali. HAU; Kiɗime (Tana nufin gigicewa ko shiga wani hali)  
1 27 28 29 30 31 34