Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
College - A turance tana nufin kwaleji.
Misali; Duk wanda zai shiga kwaleji sai ya yi jarrabawa.
HAU; Kwaleji (Tana nufin makarantar gaba da firamare ko gaba da sakandire)
College - A turance tana nufin kwaleji.
Misali; Idan matasa suka shiga kwaleji suna jin kansu.
HAU; Kwaleji (Tana nufin makaranta musamman ta gaba da sakandire)
Colleges of Education Academic Staff Union (CEASU) - Ƙungiyar malaman kwalejojin ilimi
Collision - A turance tana nufin karo.
Misali; Karo na yi da bango saboda duhu, shi yasa goshi na ya kumbura.
HAU; Karo (Tana nufin haɗuwar ba-zata)
Comission on things sold - A turance tana nufin kamasho.
Misali; Mukan samu kamasho a kowanne kaya da aka siyar a shago.
HAU; Kamasho (Tana nufin wani kaso na kuɗi da ake samu bayan an yi ciniki)
Commission - Hukuma, Kwamiti
Common Sense - A turance tana nufin kan-gado.
Misali; Yaron yana da kan-gado ainun.
HAU; Kan-gado (Tana nufin hankali ko fahimta)
Communal Work - A turance tana nufin gayya.
Misali; Samarin yankin na yin aikin gayya a kowane mako.
HAU; Gayya (Tana nufin taro ko mutane da yawa)
Company - A turance tana nufin kamfani.
Misali; Alhaji Mudi ya gina sabon kamfani a karkararsu.
HAU; Kamfani (Tana nufin ma'aikata mai ɗauke da mutanen da suke aiki a ƙarƙashinta)
Compare - A turance tana nufin kamanta.
Misali; Alƙalin yana kamanta adalci a shari'o'insa.
HAU; Kamanta (Tana nufin kwantantawa)