Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Cocin ECWA/ Cocin Ƴaɗa Kiristanci Ta Yammacin Afirka - Evangelical Church of West Africa (ECWA)
Cock Crow - A turance tana nufin cara.
Misali; Tun da zakara ya yi cara na farka.
HAU; Cara (Tana nufin kukan da zakara yake yi musamman da asuba)
Cocky young person who wears western dress - A turance tana nufin gaye.
Misali; Ai yanzu ya zama gaye, kullum za ka gan shi da shigar nasara.
ENG; Gaye (Tana nufin matashi wanda yake shiga irin ta turawa)
Coco-yam - A turance tana nufin gwaza.
Misali; Na gamu da mai siyar da gwaza da fita kasuwa.
HAU; Gwaza (Tana nufin makani)
Cocoa Reserch Institute of Nigeria (CRIN) - Cibiyar Binciken koko Ta Nejeriya
Coconut - A turance tana nufin kwakwa.
Misali; Kunun kwakwa na da matuƙar daɗi da ƙara lafiya.
HAU; Kwakwa (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan marmari mai mutuƙar amfani ga ɗan Adam)
Cocumber-like Vegetable - A turance tana nufin gurji.
Misali; Gurji yana da daɗi idan an kwaɗanta shi da ƙuli-ƙuli.
HAU; Gurji (Tana nufin wani nau'i na kayan lambu mai kama da kwakunba amma ya fi ta girma)
Code of Conduct Bureau (CCB) - Hukumar ɗa'ar ma'aikata
Cold - A turance tana nufin hunturu.
Misali; Lokacin hunturu akan kunna wuta domin jin ɗumi.
HAU; Hunturu (Tana nufin lokacin sanyi)
Collar - A turance tana nufin kwala.
Misali; Yana sanye ne da riga mai kwala launin shuɗi.
HAU; Kwala (Tana nufin wuyan riga irin ta Bature)