Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ciyawa - Tana nufin tsiron da yake fitowa ba tare an shuka shi ba, tana da siraran ganye koraye.
Misali;Ciyawa ta fito a gonar sosai, dole sai an cire ta kafin yi shuka.
ENG; Grass (A turance tana nufin ciyawa)
Clearly - A turance tana nufin dalla-dalla.
Misali; Malamin yana bayani dalla-dalla ga ɗalibansa.
HAU; Dalla-dalla (Tana nufin yin abu daki-daki a bayyane)
Clock/Watch - A turance yana nufin agogo.
Misali; Na siyo sabon agogo a kasuwa.
HAU; Agogo (Yana nufin manunin lokaci)
Clove - A turance tana nufin kanumfari.
Misali; Shayi idan an sa kanumfari ya fi daɗi.
HAU; Kanumfari (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan ƙamshi)
Club - A turance tana nufin kulob.
Misali; Jibrin ɗan ƙungiyar Hausa ne a makaranta.
HAU; Kulob (Tana nufin ƙungiya)
Co-wife - A turance tana nufin kishiya.
Misali; An yi wa Lantana kishiya satin da ya wuce.
HAU; Kishiya (Tana nufin abokiyar zama wadda aure ya haɗa, ma'ana idan mutum yana da mata biyu, ɗaya kishiyar ɗaya ce)
Coalition of Northern Youth Groups (CNYG) - Gamayyar ƙungiyoyin matasan Arewa
Coalition of Northern Youth Groups (CNYG) - Gamayyar ƙungiyoyin matasan Arewa
Cocin ECWA/ Cocin Ƴaɗa Kiristanci Ta Yammacin Afirka - Evangelical Church of West Africa (ECWA)
Cock Crow - A turance tana nufin cara.
Misali; Tun da zakara ya yi cara na farka.
HAU; Cara (Tana nufin kukan da zakara yake yi musamman da asuba)