Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Circumcision - A turance tana nufin kaciya. Misali; Yara shida aka yi wa kaciya a gidan. HAU; Kaciya (Tana nufin cire fata daga jikin al'aurar namiji)
Ciroma - Tana nufin sarautar da ake ba wa ɗan sarki. Misali; An naɗa yarima a matsayin ciroma jiya bayan la'asar. ENG; A traditional title usually held by son of an emir (A turance tana nufin ciroma)
Citta - Tana nufin ɗaya daga cikin sinadaran abinci mai inganci ga lafiya, tana da yaji, kuma akwai ɗanya akwai busasshiya. Misali; An zuba wadatacciyar citta a yajin. ENG; Ginger (A turance tana nufin citta)
Civil Service Commission (CSC) - Hukumar ma'aikatan gwamnti
Civil Service Commission (CSC) - Hukumar ma'aikatan Gwamnati
Civil Society Organizations (CSO) - Gamayyar ƙungiyoyin sa-kai
Civilian - A turance tana nufin farar-hula. Misali; A Najeriya mulkin farar-hula ake yi. ENG;  Farar-Hula (Tana nufin wanda ba soja ko mai ɗamara ba) Kishiyarta; Soja
Civilian Joint Task Force (CJTF) - Rundunar mayaƙan sa-kai
Civilian Joint Task Force (CJTF) - Rundunar mayakan sa-kai
Civilian Society Organizations (CSO) - Gamayyar Ƙungiyoyin Sa-Kai
1 23 24 25 26 27 34