Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Cida - Tana nufin rugugin tsawa yayin da ake ruwan sama.
Misali; Ruwa ake da cida tun da safe har ga shi yamma ta yi.
ENG; Thunder Rumbling (A turance tana nufin cida)
Cifjoji - Tana nufin alƙalin alƙalai.
Misali; Ai wanda ya yi mana shari'ar cifjoji ne, kuma ya kwatanta adalci.
ENG; Chief Judge (A turance tana nufin cifjoji)
Ciko - Tana nufin ƙara biyan kuɗi.
Misali; Da na siyo kayan sai da na yi ciko, saboda sun tashi.
ENG:Balance/ Outstanding (A turance tana nufin ciko)
Cimaka - Abincin da ake ci domin rayuwa.
Cincirindo - Tana nufin taruwar mutane da yawa.
Misali; Mutane sun yi cincirindo a ƙofar gidan sarki.
ENG;Dense Crowd (A turance tana nufin cincirindo)
Cindo - Tana nufin wanda aka haifa da yatsu shida.
Misali; Jaririn da Latana ta haifa yana da cindo.
ENG; Person with sixth finger (A turance tana nufin cindo)
Ciniyar Ƙwararrun AKantoci Ta Najeriya - Instutite Of Chartered Acoountants Of Nigeria (ICAN)
Cinnaka - Tana nufin ɗan ƙaramin baƙin ƙwaro, yana cizo mai zafi.
Misali; Idan cinnaka ya ciji mutum gurin har ɗan kumbura yake.
ENG; Small black biting ant (A turance tana nufin cinnaka)
Circle - A turance tana nufin da'ira.
Misali; Yara sun yi da'ira suna wasa.
HAU; Da'ira (Tana nufin zagayayye)
Circle the Ka’aba at Macca - A turance tana nufin ɗawafi.
Misali; Duk wanda ya je Umara sai ya yi ɗawafi.
HAU; Ɗawafi (Tana nufin zagaye Ka'aba da zimmar ibada)