Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Christian Council of Nigeria (CCN) - majalisar kiristocin Najeriya
Christian Council of Nigeria (CCN) - Majilisar Kiristocin Najeriya
Christmas - A turance tana nufin kirsimeti.
Misali; Kiristoci na bikin kirsimeti a duk ranar 25 ga watan Disamba.
HAU; Kirsimeti (Tana nufin bikin zagayowar ranar haihuwar Yesu Almasihu)
Ci-rani - Tana nufin barin gari da zimmar zuwa wani garin don neman kuɗi musamman a lokacin rani.
Misali; Samarin ƙauyen duk sun tafi ci-rani, sai damina ta kusa sauka suke dawowa.
ENG; Going away from home during the dry season in search of work (A turance tana nufin ci-rani)
Cibi - Tana nufin cokali.
Misali; A Sokoto cibi ake kiran cokali.
ENG; Spoon (A turance tana nufin cibi)
Cibiya - Tana nufin sashen jiki da ke tsakanin ciki da mara.
Misali; Jaririn yana da cibiya babba, sai an gasa masa sosai.
ENG; Navel (A turance tana nufin cibiya)
Cibiyar Aiwataccen llimi Tattali Ta Afirka - Afican Institute for Applied Economics (AlAE)
Cibiyar Akantocin Bincike Ta Najeriya - Institute of Forensic Accountants of Nigeria (IFA)
Cibiyar Akantocin Kamfani da Kasuwanci Ta Najeriya - Institute of Company & Commercial Accountants of Nigeria (ICCA)
Cibiyar Binciken Bisashe Ta Duniya - International Livestock Research Instutite (ILRI)