Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Wish - A turance tana nufin buri.
Misali; Zuwa ƙasa mai tsarki shi ne babban buri na.
HAU; Buri (Tana nufin abinda mutum yake so ya cimma)
With - A turance tana nufin da.
Misali; Ni da yayana farare ne.
HAU; Da (Tana nufin tare)
Without - A turance tana nufin babu.
Misali; Babu kaya a cikin akwatin.
HAU; Babu (Tana nufin wayam ko ba komai)
Woman’s Head-tie - A turance tana nufin kallabi.
Misali; Ƙanwata ta iya ɗaura kallabi.
HAU; Kallabi (Tana nufin ɗan kwali ko fatala)
Woman’s Large Wrapper - A turance tana nufin gyauto.
Misali; Ta ɗaura gyauto mai matuƙar kyau da tsada.
HAU; Gyauto (Tana nufin babban zani na mata)
Woman’s Shawl - A turance tana nufin gyale.
Misali; Kande ta yafa sabon gyale.
HAU; Gyale (Tana nufin mayafi ko abin rufe jiki na mata)
Woman’s Underskirt - A turance tana nufin fatari.
Misali; Ta shanya fatari a igiya bayan ta wanke.
HAU; Fatari (Tana nufin siket ɗin da mata suke sa wa a ƙasan kaya)
Women Trafficking & Child Labour Eradication Foundation (WOTCLEF) - Kadaurar Daƙile Safarar Mata da Bautar da Yara
Wood - A turance tana nufin icce.
Misali; Idan aka samu icce busasshe wuta tana saurin kamawa.
HAU; Icce (Tana nufin reshe ko gangar jikin bishiya da ake amfani da shi wajen hura wuta a yi girki)
Words/Speech - A turance tana nufin kalami.
Misali; Ya iya kalami mai daɗi shi yasa mutane ke son shi.
HAU; Kalami (Tana nufin zance ko magana)