Mene Ne Amfanin Zumunci?

0
2458

Sadar da zuminci,shi ne ziyarar ‘yan uwa da dangi da abokai na alkhairi da taimakon su da agaza musu.

Annabi (S.A.W) ya bayyana mana sadar da zumunci da cewa hanya ce ta samun arziƙi da rayuwa mai daɗi a nan duniya da Lahira.

Sai ya ce:
(ﻣَﻦْ ﺳَﺮَّﻩُ ﺃَﻥْ ﻳُﺒْﺴَﻂَ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﺭِﺯْﻗُﻪُ، ﺃَﻭْ ﻳُﻨْﺴَﺄَ ﻓِﻲ ﺃَﺛَﺮِﻩِ ، ﻓَﻠْﻴَﺼِﻞْ ﺭَﺣِﻤَﻪُ)

Duk wanda yake son Allah ya yalwata arziƙinsa kuma ya tsawaita rayuwarsa, to
ya sadar da zumincinsa).
@ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏) 2067 ‏( ،ﻭﻣﺴﻠﻢ ‏) 2557 ‏( ،ﻭﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ‏) 1693 )

A wani Hadisin yana cewa:
(ﺍﻟﺮَّﺣِﻢُ ﻣُﻌَﻠَّﻘَﺔٌ ﺑِﺎﻟْﻌَﺮْﺵِ ﺗَﻘُﻮﻝُ ﻣَﻦْ ﻭَﺻَﻠَﻨِﻲ ﻭَﺻَﻠَﻪُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻭَﻣَﻦْ ﻗَﻄَﻌَﻨِﻲ ﻗَﻄَﻌَﻪُ ﺍﻟﻠَّﻪ)

(Zumunci yana rataye a jikin al’arshi, yana cewa, ya Allah ka sadar da wanda ya sadar da ni, ka yanke wanda ya yanke ni).
@ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏) 5989 ‏( ﻣﺴﻠﻢ ‏)

Mu haɗu a darasi na gaba insha Allah.

labarin da ya wuceCiwon Mara Lokacin Al’ada
Labarin na GabaLadubban Tarewa A Gidan Miji
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.