Zirga-Zirga Tsakanin Bokaye Da Masu Duba Don Neman Duniya

0
689

Na lura cewa duk lokacin da aka sami kai ƙarƙashin mulkin farar hula, tabbas kasuwar bokanci da duba tana buɗewa, ta yi ta ci ba ƙaƙƙautawa, inda za ka ga masu neman duniya maza da mata suna zarya da zirga-zirga da cincirindo zuwa wajan bokaye da ‘yan duba, ga shi kuwa bokanci da duba haramun ne ga musulmi, sawa’un za a yi wa ko kuwa shi zai yi wa wani
Allah (Subhanahu wata’ala) ya ce:

Ma’ana “…. (Annabin Allah) Sulaimanu bai kafirta ba, sai dai shaiɗanun da suke sanar da mutane tsafi su ne suka kafirta….” Baƙara (102).
Kuma Imam Muslim ya rawaici hadisi da aka karɓo daga Hafsa Allah ya yarda da ita daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Duk wanda ya je wajen wani mai tutiyar sanin abubuwa kafin faruwar su, sai ya tambaye shi game da wani abu, to ba za a karɓi sallarsa ba, har tsawon kwana arba’in.”
Idan kuwa har musulmi ya kuskura ya gasgata abin da boka da ɗan-duba ya gaya masa, to , ya ɓarar da imaninsa. Dalili kuwa an karɓo hadisi daga Abu Huraira, Allah ya yarda da shi, daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce:“Duk wanda ya je wajan boka kuma ya gasgata shi game da abin da yake faɗa, to haƙiƙa, ya kafirce wa abin da aka saukar wa Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) .”
Abu Dawud, Tirmizi, Ibn Majah, da wasunsu ne suka rawaito shi.
Don haka zartar wa kai zuwa wajen boka ko dan-duba saboda neman kujerar shugabancin ƙasa, ko ta gwamna, ko ta ɗan majalisa, ko ta ciyaman ko don neman zarcewa a kan wani matsayi, ba ƙaramin kantafi da Imani ba ne ga musulmi.
Bayan haka, ni kiranmu ga ‘yan’uwa musulmai a duk lokacin da muka tashi neman wani abin ƙaruwa, to mu yi ƙoƙari mu bi hanyar da muka san ba a saɓawa dokokin addininmu ba.

sannan kuma a kodayaushe a zuci mu rinƙa halarto da bayanan Manzo (Sallallahu Alaihi Wasallam) masu zuwa kamar haka:

1. Faɗin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa: “Haƙiƙa kowanne ɗayanku ana tattara halittarsa a cikin mahaifiyarsa (ya) kwana arba’in yana maniyyi, sannan ya zama gudan jini kwatankwacin haka, sannan a gudan tsoka kwatankwacin haka, sannan a aiko mala’ika zuwa gare shi ya busa masa rai, kuma a umarci mala’ikan da rubuta arzikinsa da aikinsa da lokacin mutuwarsa da zamantowar sa musulmi ko kafiri…”
2. Faɗin Manzo (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa: “Ka sani haƙiƙa, duk abin da ya kuskure maka da ma can Allah bai yi zai same ka ba, kuma duk abin da ya same ka da man can Allah bai yi zai kuskure maka ba.”
Imam Ahmad da wasunsu ne suka rawaito shi.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Hattara Dai ‘Yan Siyasa Musulmai wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceFifita Sila Da Sanadin Faruwar Abu Fiye Da Hukuncin Allah Da Ƙaddararsa
Labarin na GabaAikin Uba