Yin Afuwa Da Kyautatawa Wanda Ya Ɓata Maka

0
21

Tsakanin harshe da haƙori ma akan saɓa ballantana tsakanin mutum da mutum, kuma duk wanda ya ce: “Zo mu zauna, ya ce zo mu ɓata. Waɗannan kalmomi ne na hikima masu ɗauke da darussa na rayuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali. 

To magani shi ne saba wa da haƙuri da yin afuwa, saboda tilas sai ka ga yadda ba ka so, in kuwa ka ce duk abinda aka yi maka sai ka rama, to lallai wata rana za ka rame. Yin afuwa yana janyo wa mutum mutumci, kwarjini, farin jini, lada da farin ciki da kwanciyar hankali. Ga waɗansu ‘yan misalai: 

Waɗansu miyagun malamai sun taɓa haɗe wa Shaihul Islam Ibn Taimiyya kai, suka yi ta cutar sa, har suka yi masa sharri, aka jefa shi a kurkuku. Lokacin da aka sake shi, sai aka tambaye shi ko kana tunanin ɗaukar fansa? Sai ya ce: 

“A’a duk na yafe musu ba komai, Allah ya saka musu da alhairi, zaman kurkuku yasa na yi nazarin Kur’anina, na fahimci waɗansu abubuwa da dama, kuma ai su ne sanadi, na yi musu afuwa, ba wani abu”. 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

Wani bawan Allah ya sami labarin cewa, wani mutum ya yi da shi, ya ci zarafinsa. Sai ya ɗauki goma ta arziƙi ya tafi da kansa ya kai masa har gida. Sai mutumin ya tambaye shi dalilin wannan alhairi. Sai ya ce, “Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Wanda ya yi muku alhairi, ku saka masa.” 

To kai ka ba ni kyautar ladan ayyukanka, ni kuma ba ni da wani abin da zan saka maka da shi sai ɗan wannan abin a duniyar nan. Allahu Akbar. Ɗan uwa ka ɗauki dabi’ar afuwa ga iyalanka, maƙotanka, da sauran al’umma ka ga yadda za ka zauna lafiya, ka samu nutsuwa. 

DADDAƊAR MAGANA 

Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Wanda ya yi imani da Allah da ranar Lahira ya faɗi alhairi ko ya yi shiru. 

Duk mutumin da yake aiki da wannan hadisi haƙiƙa zai zauna lafiya da kowä, kuma zai samu kwanciyar hankali. Duk abin da zai fito daga bakinka, ya kasance alhairi ne, magana ce ta gaskiya mai daɗi, wacce ba za ta bata wa kowa ba.

Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

ADDU’A 

Komai ya yi zafi maganinsa Allah. Kuma addu’a makamin mumini ce. Saboda haka, bayan bin waɗannan mataki da sauran su, sai ka kasance kullum cikin roƙon Allah ya ba ka zaman lafiya da kwanciyar hankali. Musamman ka riƙi addu’o’in zaman lafiya na Manzon Allah (S.A.W) kamar wannan adda’ar. 

Domin Karanta Cikakken Bayanin Abubuwan Da Sai Da Su Aure Yake Zama Karɓaɓɓe Danna Nan

Allahumma aslih lii diini allazi kuwa ismatu amri, wa aslhh Ii dunyaa ya allati fiha ma aashi wa aslih lii aakhirati allati fihaa ma aadi, waj alil hayaata ziyaada talli fi kulli hairin waj alil mauta raahatalli min kulli sharrin. Allahuma rahmataka arju fa laa takilni ila nafsi tarlata ainin wa aslih lii sha’ani kullihi laa ilaaha illa anta. Allahuma inni a ‘uzu bika mnial hammi wal hazani wa minal jubni, wal bukhli, wa min hazani wa minal jubni, wal bukhli, wa min galabatid daini wa kahriijaal. 

Waɗannan kaɗan kenan daga abubuwan da suke wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. A dunƙule za mu iya cewa bin Allah da Manzonsa sau da ƙafa da tsarkake zuciya da jiki da mazauni da bai wa ƙwaƙwalwa lafiyayyen abincin imani da kyakkyawar niyya, su ne kaɗai za su kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali. Allah ya sa mu da ce. Amin. 

Bayan waɗannan fa’idoji, malamai musamman masana halin ɗan Adam suna bayyana waɗansu ladabai ko dabaru domin zaman lafiya da mutane iri-iri. Koda yake waɗannan ƙa’idoji da suka gabata sun isa ga duk mai son zaman lafiya da kwanciyar hankali ya rayu da su, amma duk da haka, akwai waɗansu abubuwa da masana suka yi bayani, Ina ganin ya kamata a kammala wannan littafi da su.

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceMenene Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali?
Labarin na GabaMaganin Farin Jini