Yadda Za Ki Nunawa Mijinki Tsantsar Kula

0
88

A kowacce irin alaƙa ana buƙatar juriya. Hanyoyin da ya kamata ki bi wajen samarwa da gidan aurenki zaman lafiya shi ne ta hanyar nuna kulawa ga mijinki

kamar haka:

1.MIJINKI YA ZAMTO YANA IYA BAYYANA DAMUWARSA A GARE KI

Mazaje da yawa sukan samu matsaloli wanda ba sa iya bayyanar da su ga kowa sai dai su bar abun a ransu. Ki kasance mai samar da wani lokaci wanda za ku kasance ku kaɗai domin bayyanar da damuwarku ga juna.

Karanta Abubuwan Daya Dace A Sani Akan Allurar Artemether

2.TAMBAYAR MIJINKI GAME DA BUƘATUN SA 

Mutane da dama sukan kasa samun yadda za su bayyana damuwarsu har sai sun samu mai tambayarsu. Yana da kyau ki kasance mai iya magana ta hanyar tuntuɓar mijinki akan halin da yake ciki idan kin gan shi a wani yanayi ta haka ne zai samu damar amayar da abunda yake ransa.

3.KYAKKYAWAR MU’AMALA

A duk lokacin da ɗayanku yake buƙatar yin wani abu ya kamata ya samar da ɗan uwansa domin samun daidaito.

Domin karanta bayani akan Vaginal Infection shiga nan

labarin da ya wuceYadda Za Ki Kula Da Fatarki
Labarin na GabaYadda Zaki Sa Mijinki Ya Qara Sonki
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.